✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta harbi karin mutum 1133, ta kashe wasu 5 a Najeriya

An samu karin mutum 1,133 da cutar Coronavirus ta harba yayin da kuma ta kashe karin mutum 5 a fadin Najeriya. Hukumar NCDC mai YaKi…

An samu karin mutum 1,133 da cutar Coronavirus ta harba yayin da kuma ta kashe karin mutum 5 a fadin Najeriya.

Hukumar NCDC mai YaKi da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasar ce ta sanar da hakan ranar Laraba cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Alkaluman sun nuna san samun karin mutum 1,236 da cutar ta harba a jihohi 18 da suka hada Legas (397), Abuja (357), Kaduna (81), Filato (63), Katsina (46), Sakkwato (32), Oyo (28) da Ogun (21).

Sauran su ne Kano (19), Ribas (18), Osun (13), Edo (12), Neja (12), Bayelsa (11), Borno (11), Bauchi (8), Jigawa (2), da Ondo (2).

Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 80,922 a fadin Najeriya yayin da kuma an sallami mutum 69,274 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka.

Kazalika, a jimillance alkaluman sun nuna cutar ta kasha mutum 1,236 a fadin kasar tun daga bullarta a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu.