Mai Martaba Olubadan Oba Saliu Adetunji ya umarci dodannin da suka saba fitowa gudanar da bukukuwan al’ada a kowace shekara da kada su fito a bana domin guje wa yaduwar cutar coronavirus a tsakanin jama’a.
Sarkin ya bukaci shugabannin dodannin su gudanar da bukukuwan nasu a cikin gidajensu na al’ada ba tare da yawo a cikin gari ba.
Olubadan ya bayar da umarnin ne cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kuma Daraktan Labarai a fadarsa Mista Adeola Oloko ya sanya wa hannu da aka raba wa ‘yan jarida a ranar Lahadi.
Coronavirus: Za a yi wa matafiya 11 gwaji a Ibadan kafin a mika su Sokoto
Gwamnan Oyo ya yi wa alu’ummar Sabo Ibadan ta’aziyya
Sanarwar ta ce Olubadan da hadin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki musamman Gwamnatin Jihar Oyo da Rundunonin tsaro sun amince da hana dodannin gudanar da bikin Egungun Festival na bana da aka shirya yi a mako mai zuwa.
Sarkin ya kuma yi kira ga al’ummar Masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 da su yi aiki da shawarar mahukumta wajen yin amfani da abubuwan kariya daga cutar coronavirus da suka hadar da yawan wanke hannu da sanya kyallen rufe baki da hanci da nisantar juna a wuraren taruwar jama’a.
Yadda ake wasan dodanni.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa dodannin na fara fitowa ne daga gidajensu na al’ada da sassan jikinsu da fuskokinsu a lullube, suna tafe mabiyansu na musu kad-kade da raye-raye da wakokin al’ada.
Dodannin da mabiyansu kan shafe kwanaki 5 zuwa 7 suna yawon ziyartar sassa daban-daban na birnin Ibadan kafin su koma gidajen al’ada.
Shin mata na hada ido da dodo?
Binciken ya nuna bisa al’ada, daya daga cikin dodannin mai suna Ololu idan ya fito cikin gari, to duk matar da ta hada ido da shi za ta mutu.
Wannan ne ya sa mata ke kukkulle kansu a cikin gidaje domin guje wa yin ido biyu da Ololu saboda tsoron mutuwa ta dalilin hada ido da shi.
Rikici ya barke saboda kallon dodo
A shekarun baya, a daidai lokacin da Ololu ya fito ne wani malamin Mususlunci ya debi matansa da ‘ya’yansa mata ya kai su suka yi ido hudu da dodon a inda yake yawo a gari ba tare da komai ya same iyalen malamin ba.
Wannan al’amari ya haifar da rikici tsakanin mabiyan malamin da mabiyan Ololu.
Sai dai jami’an tsaro sun yi hanzarin daukar matakin hana kazantar rikicin a wancan lokaci.
Olubadan, Oba Saliu Adetunji ya yi kira ga dodannin su bayar da gudunmawarsu wajen yin addu’o’in maganin annobar coronavirus a Najeriya.