Ranar Alhamis ne umarnin da Gwamnatin Jihar Legas ta bayar na rufe kasuwanni zai fara aiki a matsayin matakin da ake ci gaba da dauka domin hana yaduwar cutar Coronavirus.
A cikin makon nan ne gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umarnin rufe wasu kasuwannin jihar ban da kasuwannin da ake sayar da kayan abinci da magunguna ko ruwan sha.
Kasuwannin da umarnin na gwamnatin Legas ya shafa su ne:
- Babbar kasuwar sayar da wayoyin salula da dangoginta ta Computer Village da ke Ikeja wato kasuwar GSM village.
- Kasuwar Mandilaz da ke cikin garin Legas
3. Kasuwar Oluwale da ke cikin garin Legas
- Kasuwar Ogba
- Kasuwar Ladipo da ake sayar da kayan motoci
- Kasuwar Arena da ke Oshodi
- Daukacin Kasuwar Oshodi
- Kasuwar Lawason
- Kasuwar Gatankowa
- Kasuwar kayan lantarki ta duniya da ke Alaba wato Alaba International Market
- Kasuwar Baje Koli wato Trade Fair Market
- Kasuwar Igando da Alimosho, da ta Abule-egba
- Kasuwar Ebute Ero
- Kasuwar Computer Village da ke Ikeja
- Kasuwar Balogun da ke cikin birnin Lagos
- Kasuwar Iyana-Ipaja
- Kasuwar Agege
Gwaamnatin ta bayar da umarnin rufe wadannan kasuwanni ne domin rage cunkoson jama’a a birnin Legas.
Jihar Legas ita ce jihar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.