✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Sababbin ka’idojin kula da kuma sallamar masu ita

Najeriya ta sanar da sababbin ka’idojin da za a yi la’akari da su wajen gano ko ya dace a sallami mai fama da cutar coronavirus. …

Najeriya ta sanar da sababbin ka’idojin da za a yi la’akari da su wajen gano ko ya dace a sallami mai fama da cutar coronavirus. 

Matakin na zuwa ne bayan nazarin kimiyyar da ya nuna tsawon lokacin da masu dauke da cutar za su iya harbar wasu da ita.

Za a iya sallamar masu fama da cutar, kwana 10 bayan alamunta sun fara bayyana a jikinsu da kuma bayan kwana uku ba tare da alamunta ya bayyana a jikinsu ba – biyo bayan harbuwa da ita da suka yi, kamar yadda sababbin ka’idojin suka nuna.

Sai dai kuma wadanda suka kamu da cutar amma ba tare da sun nuna alamunta a jikinsu ba, za a iya sallamar su bayan kwana 14 – bayan gwajin kwayar cutar ya nuna sun sake kamuwa da cutar daga baya.

“A yanzu ba sai mun jira samun sakamakon cutar ta kau daga jikin wanda ya kamu da ita ba – kafin mu sallame shi. Muna da kwarin gwiwa mutum zai iya komawa gida ba tare da ita ko kuma sanya iyalansa cikin hadari ba,” kamar yadda Babban Darakta na Hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya – ya shaida wa Kwamitin Ko ta Kwana kan Yaki da Cutar Coronavirus, a ranar Alhamis.

“Idan kuma har alamun cutar sun dade a jikinka, to a nan za mu yi jimirin kula da kai yayin da muke maka magani,” inji Ihekweazu.

Wannan dai shi ne na uku a jerin ka’idojin yaki da cutar COVID-19 – wanda kuma ya yi nazari kan masu fama da cutar kashi biyu – watau wadanda suka nuna alamunta bayan sun harbu da kwayar cutar da kuma wadanda ba su nuna alamunta ba duk da cewa sun harbu da ita.

“Masu cutar da suka nuna alamunta a jikinsu, za a iya sallamar su akalla kwana 10 bayan bayyanar alamunta sun fara bayyana a jikinsu, ko kuma idan suka yi kwana uku ba tare da sake nuna alamunta ba; su kuma wadanda ba sa nuna alamunta za a sallame su ne bayan kwana 14 da gwajin farko da ya nuna sun kamu.

Ya ce ko da yake likitoci na dari-dari da wadannan sabbin ka’idojin, amma ya tabbatar musu cewa ka’idar tana bisa turba mai kyau.

“Don haka muna da kwarin gwiwa game da tasirin ka’idajojin, sauyi na da matukar wuyar sha’ani, saboda a baya mun kasance muna fadar cewa lallai sai sakamakon gwaji ya nuna ka warke… amma duk da cewa mun wallafa sakamakon, amma har yanzu likitoci suna dari-dari wajen aiki da sakamakon,” inji shi.

Ihekweazu ya kuma ce cibiyar NCDCn ta soke amfani da magunguna kashe kwayar cutar virus kamar su Chloroquine da hydroxychloroquine, daga tsarin magungunan da ake amfani da su wajen magance cutar.

Ya ce a yanzu za a takaita amfani da magungunan ne wajen gwaji kuma sannu a hankali, saboda rashin tabbas kan sahihancin lafiyar amfani da su.

“Tsarin da ake bi wajen magance cutar har yanzu yana nan – watau na lura da alamun cutar da na gabanin ta yi karfi a jiki da amfani da taimaka wa shakar iska da yaki da shigar kwayoyin cuta tare da tabbatar da masu fama da cutar suna samun abinci da ruwa mai kyau,” inji shi.