✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Oyo za ta mayar da tallafin shinkafa

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta mayar da buhunan shinkafa 1,800 da gwamnatin tarayya ta mika mata ta hannun Hukumar Yaki da Fasa Kwauri…

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta mayar da buhunan shinkafa 1,800 da gwamnatin tarayya ta mika mata ta hannun Hukumar Yaki da Fasa Kwauri shiyyar jihohin Oyo da Osun don rabawa a matsayin tallafi.

Mai ba gwamna shawara a kan harkokin kasuwancin kayan gona Dokta Debo Akande ya ce gwamnati ta yanke shawarar mayar da shinkafar ne bayan Kwamitin Rabon Kayan Tallafin ya gano cewa rubabbiya ce wadda bai kamata mutane su yi amfani da ita a matsayin abinci ba.

Dokta Akande, wanda tun farko shi ya karbi buhunan shinkafar a madadin gwamnatin jihar, ya kuma ce za a mayar da rubabbiyar shinkafar ne ga rundunar ta Kwastam mai kula da jihohin Oyo da Osun da fatan za ta musanya ta da mai kyau wadda mutane za su iya ci a matsayin abinci.

Ya kara da cewa mayar da wannan shinkafa ba zai shafi aikin rabon tallafin kayan abinci ga jama’a da gwamnatin jihar za ta fara nan ba da dadewa ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ne dai ya bai wa hukumar ta Kwastam umarni fitar da kayan abincin da ke jiye a rumbunanta a raba ga jama’a domin rage radadin dokar hana fita da aka ayyana da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.