Gwamnan jihar Filato kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar annobar Coronavirus a jihar, Simon Lalong ya tabbatar da cewa an samu mutum na farko da ya rasu, bayan kamu da wannan cuta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar, kan matakan da gwamnatin jihar ta dauka, na kare yaduwar wannan annoba, a yammacin ranar Lahadi.
Gwamnan ya yi bayanin cewa a ranar Asabar aka dauki jinin wannan mutum da ya rasu, domin aje a yi gwajin wannan annoba, amma kafin sakamakon gwajin ya fito ya rasu.
- COVID-19: Gwamnatin Filato ta sassauta dokar hana fita
- Coronavirus: Gwamnatin Filato ta rufe iyakokin jihar
- COVID-19: An sallami mutum 10 a Plateau
Gwamnatin jihar ta sallami wasu
Gwamna Simon ya ce an sallami mutum 10 da suke dauke da wannan annoba a jihar, bayan da aka yi masu gwaji aka tabbatar sun warke.
Don haka tuni aka sallame su, suka koma cikin iyalansu.
”An dada sassauta dokar kulle a jihar nan, zuwa kwanaki hudu a mako, maimakon kwanaki uku. Don haka daga wannan makon za a sassauta dokar, daga ranakun Alhamis da Juma’a da Asabar da Lahadi.
Daga nan kuma dokar ta ci gaba da aiki, a ranakun Litinin da Talata da Laraba. Gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne, domin ta dada sassautawa al’ummar jihar, kan mawuyacin halin da aka shiga, sakamakon daukar wadannan matakai”.
Gwamnan ya yi bayanin cewa babban kalubalen da ake fuskanta a jihar, shi ne yadda ake karya dokar rufe kan iyakokin jihar, ta yadda mutane suke shigowa jihar, ta wasu hanyoyin dazuzzuka daga wasu jihohi.
”Wannan babban hadari ne ga jihar kan wannan cuta domin dukkan wadanda suke dauke da wannan cuta a jihar, sun fito ne daga wasu jihohi.“ In ji Gwamnan.
Za a rufe kasuwa saboda karya doka
Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar zata rufe kasuwar ’yan tumatur ta Farar Gada da ke garin Jos, saboda karya dokokin kare yaduwar wannan cuta na jama’a su nesanta da juna da rashin tsafta.
A cewar Gwamnan idan aka rufe kasuwar ba za a sake budeta ba har sai shugabannin kasuwar da shugabannin karamar hukumar Jos ta Arewa sun kawo gamsasshen tsarin kiwon lafiyar da aka yi a wannan kasuwa.
Har’ila yau, ya ce rufe kasuwannin cikin garin Jos da gwamnatin tayi sakamakon gujewa yaduwar wannan annoba yana nan.