Gwamna Abubakar Atiku-Bagudu na jihar Kebbi ya amince a biya ma’aikatan lafiya da ke bakin daga dare da rana a yakin da ake yi da coronavirus alawus na musamman.
Mai bai wa gwamnan shawara na musamman a kan al’amuran yada labarai, Malam Yahaya Sarki, ya ambato Kwamishinan Lafiya Alhaji Jaafar Mohammed yana bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi.
“An tsara wadannan alawus-alawus din ne don su inganta abin da ake biyan ma’aikatan lafiyar, a matsayin wata ‘yar sakayya saboda hadarin da suke fuskanta yayin kula da masu dauke da COVID-19.
“Ma’aikatan da abin ya shafa sun hada da jami’an kiwon lafiyar al’umma da likitoci da ma’aikatan jinya da masu harhada magunguna da kuma ma’aikatan dakin bincike.
“Sauran su ne jami’ai masu tattara bayanan bullar cuta da daraktocin kananan asibitoci a kananan hukumomi da kwararrun likitoci”, inji kwamishinan.
- Yadda ma’aikatan lafiya ke kamuwa da COVID-19 a Najeriya
- Muna cikin fargaba da damuwa —Ma’aikatan lafiya a Kano
Abin da kowa zai samu
Kwamishinan, wanda shi ne shugaban kwamitin kar-ta-kwana na yaki da CIVID-19 a jihar, ya kuma ce za a bai wa kwararrun likitoci N20,000 yayin da sauran likitoci za su rika karbar N15,000 a kullum.
“Ma’aikatan jinya da masu harhada magunguna da ma’aikatan dakin bincike za su rika karbar N10,000 a kullum yayin da direbobin motocin daukar marasa lafiya da masu share-share da masu gadi za su rika karbar N5,000 a kullum”, inji shi.
A cewar Alhajo Jaafar Mohammed, an tsara alawus-alawus din ne domin ya zamanto iya hadarin da mutum ke fuskanta iya yawan kudin da za a ba shi.
‘Yan kwamiti ma
Su ma dai mambobin kwamitin kar-ta-kwanan ba a bar su a baya ba, domin gwamnan ya amince a ba su alawus na musamman.
Ko wanne mamba na kwamitin zai samu N250,000 yayin da shugaban kwamiti zai karbi N500,000.
“Kwaraarru masu ba da shawara za a ba su N300,000, yayin da likitoci da masu harhada magunguna da ma’aikatan dakin bincike da ma’aikatan jinya da ke cibiyoyin killace mutane za a ba su N250,000 ko wanne.
“Haka ma liktoci a asibitoci wadanda aka yiwa horo a kan hana yaduwar cututtuka da kula da masu dauke da cututtuka masu yaduwa za a ba su N200,000 ko wanne yayin da ma’aikatan jinya a manyan asibitoci wadanda aka yiwa horo a kan kula da takaita cututtuka masu yaduwa za su karbi N150,000”, inji kwamishinan.
Sai dai babu bayani a kan ko kudin da mambobin kwamitin kar-ta-kwana da masu ba da shawara za su karba sau daya kawai.