Wani dan kasar Burtaniya mai shekara 66 ya mutu a jihar Legas bayan ya kamu da cutar Coronavirus.
Kwamishinan Lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar mutuwar dan Burtaniyan a shafinsa na Twitter ranar Laraba.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa, a yanzu haka masu dauke da cutar sun karu zuwa 130 a jihar. Kamar yadda ya wallafa a shafin nasa: “Jihar Legas ta sake samun karin mutum guda da ya mutum sanadiyyar cutar COVID-19 a jihar mai shekara 66, wanda ya yi tafiya daga kasar Indiya zuwa birnin Dubai sannan ya dawo Legas ranar 17 ga watan Maris, 2020.”
“A ranar 7 ga Afrilu, 2020, an samu karin mutum 10 da suka kamu da cutar COVID-19. Hakan ya sa adadin masu dauke da cutar COVID-19 a jihar Legas ya kai 130.”
A ranar Asabar 4 ga Afrilu, an samu dan Najeriya mai shekara 36 da ya rasu a Legas. Sannan an samu rahoton wani mutum mai shekara 55 da ya rasu sanadiyyar cutar Coronavirus a asibitin jami’ar jihar Legas da ke Idi-Araba.
- Coronavirus: An sallami mutum 7 a Abuja
- Coronavirus: Yadda za ku kare kanku daga mazambata
- Yawan masu Coronavirus a duniya ya haura miliyan 1