✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Bukatar gwamnati ta tallafa wa manoman Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa na bukatar ta sama wa manoma kayan noma da irin shukawa don rage tasirin da cutar coronavirus da suka fuskanta sakamakon dokar…

Gwamnatin Jihar Jigawa na bukatar ta sama wa manoma kayan noma da irin shukawa don rage tasirin da cutar coronavirus da suka fuskanta sakamakon dokar kulle.

Malami a Jami ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse (FUD) ya jaddada bukatar gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma da irin shuka mai yi da wuri kasancewar sun samu nakasun tattalin arziki sakamakon dokar da ta dakatar da harkoki.

Ado Garba Jangargari wanda masani ne a fannin noma ya ce a matsayin gwamnatin Jigawa ta manoma, akwai bukatar gwamnatin ta agaza wa masu sana’ar.

Ya kuma bayyana damuwa game da matsalolin da cutar coronavirus ta haifar wa manoma a Najeriya, wadda ya ce tayi sanadiyyar rashin yin shuka a kan lokaci.

Rashin yin shuka a kan lokaci babbar matsala ga manoma inji shi, don haka akwai bukatar gwamnati ta tallafa da kayan da manoma ke bukata a matsayin tallafin coronavirus.

Yin hakan, yana ganin zai taimaka wajen rage wa al’umma halin matsin rayuwa da ake ciki sakamakon bullar cutar.