✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An samu sabbin kamu 34

An samu mutum 34 sabbin kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya. Da take tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na…

An samu mutum 34 sabbin kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.

Da take tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu 18 daga cikin mutanen ne a jihar Legas, 12 a jihar Kano, biyu a jihar Katsina, daya a jihar Delta, daya kuma a jihar Neja.

“Zuwa karfe 11.20 na daren 15 ga watan Afrilu, an tabbatar da mutum 407 sun kamu da #COVID-19 a Najeriya; daga cikin su an salami 128, yayin da 12 suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.

A jawabin da ya yi ga al’ummar Najeriya da maraicen Litinin dai Shugaba muhammadu Buhari ya yi alkawarin inganta cibiyoyin gwajin cutar coronavirus da na killace wadanda aka tabbatar sun kamu.