✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An samu karin mutum 64 da suka kamu

  Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 64. Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu…

 

Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 64.

Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ta nuna cewa hakan ya kai adadin wadanda aka tabbatar sun kamu din zuwa 1,337.

“Zuwa karfe 11.20 na daren 27 ga watan Afrilu, an samu mutum 1,333 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya, yayin da mutum 40 suka mutu, 255 suka warke aka kuma sallame su”, inji sanarwar.

Talatin da hudu daga cikin mutanen 64 a jihar Legas suke, 15 a Babban Birnin tarayya Abuja, 11 a Borno biyu a Taraba da Gombe.