✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Adadin wadanda suka kamu ya kai 318

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 318. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce…

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 318.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter.

“Zuwa karfe 9.30 na daren 11 ga watan Afrilu, akwai mutum 318 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya. Daga cikin wannan adadin an sallami mutum 70, yayin da mutum 10 suka riga mu gidan gaskiya”.

Mutum 11 daga cikin sabbin kamuwar dai a jihar Legas suke, daya a jihar Kano, daya kuma a jihar Delta.

Wannan ne dai karo na farko da aka samu wanda ya kamu da cutar a jihar Kano, lamarin da ya sa jihohin da ke da najinyata suka kai 19.