✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Abubuwan da mutum zai ci domin kara garkuwar jiki

Akwai batutuwa da dama da suke yawo a kan cewa garkuwar jiki kan yaki kwayar cutar coronavirus da kan shi. Sai dai har yanzu ba…

Akwai batutuwa da dama da suke yawo a kan cewa garkuwar jiki kan yaki kwayar cutar coronavirus da kan shi.

Sai dai har yanzu ba a samu kwararran hujjoji ba a kan hakan, domin har yanzu yawan wanke hannu da bada rata da juna su ne hanyoyin da suka fi dacewa wajen kiyaye yaduwar cutar.

Daraktar Bangaren Cimaka da Kula da Jiki a Cibiyar Lafiya ta Boston, Cariline Apovian ta ce, “idan ka kamu da coronavirus, duk yawan lemun da za ka sha, sai ka kamo da ita.

Don haka ne ya kama a samu garkuwar jiki mai karfi kafin a kamu da cutar a matsayin rigakafi.

Don kara samun garkuwar jiki mai karfi, mun tattaro muku wasu sinadarai da za su taimaka matuka.

Bitamin C

Bitamin C yana matukar taimakawa wajen yaki da kwayar cutar mura da sanyi. Sinadarin na matukar taimakawa wajen yaki da duk wata bakuwar cuta ta hanyar karfafa garkuwar jiki. Haka kuma sinadarin Bitamin C na magance gajiya.

Kasancewa jiki ba ya iya hada sinadarin da kan shi, ko adana shi, ana bukatar mutum ya rika cin sinadarin kullum. Za a iya samun sinadarin Bitamin C daga lemu da gwanda da abarba da sauransu.

Bitamin E

Shi ma bitamin E bincike ya nuna cewa yana kara karfin garkuwar jiki, musamman ga dattawa. Ana samun bitamin E a cikin abinci da dama kamar su man giriki da nama da kwai da sauransu.

Sinadarin Zinc

A lokuta da dama a kan yi watsi da batun sinadarin Zinc idan ana batun sinadarai masu kara garkuwar jiki, amma kuma jikin mutum na bukatar shi domin yin aiki mai kyau. Ana iya samun sinadarin Zinc daga nama da kashe da hatsi da sauransu.

Bitamin A

Shi ma bitamin A yana taimakawa matuka wajen inganta garkuwar jiki. Akwai sinadarin da ake kira carotenoids, wanda shi ne yake taimakawa wajen wannan aiki.

Ana samun sinadarin na carotenoids daga karas da mangoro da gwanda da sauransu.

Sauran abubuwand da za su kara wa mutum jiki akwai dinji da tafarnuwa da sauransu.