✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Abba Kyari ya rasu

Allah Ya yi wa shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya Mallam Abba Kyari rasuwa bayan ya sha fama da jinyar cutar Coronavirus. Da misalin karfe…

Allah Ya yi wa shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya Mallam Abba Kyari rasuwa bayan ya sha fama da jinyar cutar Coronavirus.

Da misalin karfe 12.44 na daren Asabar, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Marigayin, wanda aka tabbatar da kamuwarsa da cutar bayan ya yi wani balaguro zuwa kasar Jamus, ya rasu ne a ranar Juma’a.

Mallam Kyari, wanda na hannun damar Shugaba Buhari ne, ya shafe makwanni yana jinya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Legas, kuma ana kyautata zaton a can ne ya rasu.

Shi ne babban jimi’in gwamnati na farko da ya rasu sakamakon kamuwa da cutar, wadda yanzu haka ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 17 a Najeriya.

Kusan mutum 493 aka hakikance cewa sun kamu da cutar kawo yanzu a kasar, yayin da 159 suka warke.

%d bloggers like this: