✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronabirus: Kasashen da suka tabbatar da bullar cutar a cikinsu

Ana kara samun mutane da dama a  fadin duniya da aka tabbatar sun harbu da kwayar cutar Coronabirus 2019-nCob (Cutar Kurona) – da ta samo…

Ana kara samun mutane da dama a  fadin duniya da aka tabbatar sun harbu da kwayar cutar Coronabirus 2019-nCob (Cutar Kurona) – da ta samo asali daga wata kasuwar sayar da abincin teku (Seafood) a birnin Wuhan na kasar China.

A China kanta, an tabbatar da cewa akalla  mutum 106 suka mutu yayin da fiye da  4,500 suka kamu da cutar.

An kuma samu karin kasashen a Nahiyar Asiya da Turai da Arewacin Amurka da cutar ta bulla.

Ga jerin kasashen da suka tabbatar da bullar cutar a kasarsu zuwa yanzu:

Austireliya

Kasar Austeraliya, ta tabbatar da bullar cutar a kasarta inda mutum biyar suka harbu. Na baya-baya cikinsu, ita ce wata mata mai shekara 21 wacce ta shiga jirgin karshe da ya baro birnin Wuhan zuwa Sydney – gabanin China ta rufe hanyoyin sufurin birnin.

Akwai wani mutum da ya sauka a birnin Melbourne daga China. Sai kuma wadansu maza uku a Sydney da ba su dade da dawowa daga China ba. Ana yi musu magani ne a wasu asibitocin karkara, bayan da aka kebe su.

Kambodiya

Kasar Kambodiya ma ta tabbatar da bullar cutar ga wani mutum daya a ranar Litinin.

Ministan Lafiya na kasar, Mam Bunheng, ya ce mutumin mai shekara 60 wanda dan kasar China ne a birnin Sihanoukbille da ke gabar ruwa.

Kanada

Wani mutum da ya sauka a birnin Toronto tare da matarsa ranar 22 ga Janairun  nan bayan ya ziyarci birnin Wuhan – an tabbatar da ya kamu da cutar ta Coronabirus. An kuma samu matar ita ma da kwayar cutar.

China

Zuwa ranar Talata akalla mutum 4,500 aka tabbatar sun harbu da cutar, galibinsu mazauna ciki da wajen birnin na Wuhan.

Akalla mutum 106 sun rasa rayukansu, kusan dukkansu daga Lardin Hubei. Sai dai mahukunta sun tabbatar da rasuwar mutum hudu a wasu wuraren na daban, daya a birnin Beijing sai kuma daya a birnin Shanghai.

Gwamnatin kasar ta takaita zirga-zirga a wani yunkuri na taka birki ga yaduwar cutar; ta kuma rufe wasu wuraren yawon bude-ido a daidai lokacin da yake ganiyar samun masu yawon bude-ido a shekara.

A birnin Macau, wanda matattarar ’yan caca ne da ke samun baki daga cikin kasar, an tabbatar da mutane shida sun kamu da cutar.

A Hong Kong, mutum takwas aka yi imanin sun kamu, yayin da ake zargin bazuwar cutar kan wadansu daruruwa.

Babban Jami’in Yankin Hong Kong, Carrie Lam, ya yi shelar barkewar cutar a zaman ‘cutar ta baci’ – wanda hakan ne kololuwar gargadi a birnin – tare da soke dukkan bukukuwan sabuwar shekarar gargajiya a yankin.

Faransa

An samu bullar cutar Coronabirus kan mutum uku a Faransa, wacce ta zama kasar Turai ta farko da ta samu bullar cutar.

Wani dan shekara 48 na kwance ad asibiti a birnin Bordeaud. Kwanankin baya ya ziyarci birnin Wuhan inda ya koma Faransa ta kasar Netherlands.

Wadansu ’yan shekara 30 ma’aurata ’yan China ma an kwantar da su a asibiti a birnin Paris.

Jamus

Jamus ma ta tabbatar da bullar cutar a karon farko a kasar ranar 28 ga Janairun nan, a kudancin Jihar Babaria.

“Wani mutum a lardin Starnberg ya kamu da sabuwar cutar ta Coronabirus,” inji wani Kakakin Ma’aikatar Lafiya, inda ya kara da cewa ana lura da mutumin  a wani wuri da aka kebe.

Sai dai ma’aikatar ba ta bayar da karin haske kan yadda mutumin ya kamu da cutar ba, amma ta ce “yana cikin yanayi mai kyau.”

Japan

Ranar 26 ga Janairu ne wani mai gabatar labarai na gidan telebijin din kasar, NHK, ya ambato Ma’aikatar Lafiyar kasar Japan tana cewa an samu bullar cutar a karo na hudu a gidan wani mai suna Wuhan mai kimanin shekara 46 wanda ya ziyarci Japan din domin hutu.

Hukumomin lafiya na kasar, sun ce an samu bullar cutar ce kan mutum na uku ranar 25 ga watan Janairu.

Maleysiya

Kasar Maleysiya ta tabbatar da mutum hudu sun kamu da cutar a ranar 25 ga Janairu. Sai dai dukkansu ’yan kasar China ne da suka shiga kasar daga birnin Wuhan domin hutu – sun shiga Maleysiya ce daga Singapore kwana biyu kafin kamuwarsu da cutar.

Wani dan shekara 40 da wata tsohuwa mai shekara 65 tare da wadansu yara ’yan shekara biyu da 11 suka harbu da cutar, kuma ana kula da su a wani asibitin gwamnatin kasar, kamar yadda Ministan Lafiya na kasar ya nuna.

Nepal

A kasar Nepal wani dan shekara 32 wanda ya taho daga birnin na Wuhan na China ma ya harbu da kwayar cutar.

Singapore

Kasar Singapore ta ce an samu rahotannin kamuwar mutum biyar da kwayar cutar, kuma dukkan mutanen sun taho ne daga birnin Wuhan inda suka je hutun sabuwar shekara ta gargajiya.

Koriya ta Kudu

Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta kasar Korea (KCDC) ta tabbatar da bullar cutar kan mutum na hudu ranar 27 ga watan nan, inda ta ce mutumin mai shekara 55 dan kasar ya dawo ne daga birnin Wuhan ranar 20 ga Janairu, kuma an yi masa gwaji tare da samun cutar a jikinsa.

Koriya ta bayar da rahoton bullar cutar karon farko ranar 20 ga watan nan a jikin wata mata ’yar shekara 35 da ta taho daga birnin na Wuhan.

Sri Lanka

A Sri Lanka ma, hukumomin kasar sun tabbatar da bayyanar cutar a karon farko a ranar 27 ga watan Janairun.

Taiwan

Taiwan ta ce an samu rahoton mutum biyar suka kamu da cutar zuwa yanzu a kasar, ta baya-bayan nan wata ’yar kasar  ce da ke aiki a birnin Wuhan kafin komawarta kasar ranar 20 ga Janairu.

Thailand

Thailand ta sanar da cewa cutar ta kama mutum 14 zuwa yanzu.

Sukhum Kanjanapimai, wani Babban Sakatare ne a ma’aikatar gwamantin kasar, ya ce dukkan mutum shida da aka samu da cutar ’yan China ne da ke yawon bude-ido da suka fito daga Lardin Hubei, kuma sun shiga kasar ce kwanakin baya. Dukkansu ’yan yankin Wuhan ne.

Amurka

Ita ma Amurka ba ta tsira daga cutar ba, inda ta tabbatar da mutum shida sun harbu da cutar – biyu a birnin Kaliforniya sai daidai daga jihohin Arizona da Chikago da Washington.

Bietnam

A ranar 23 ga Janairu Bietnam ta sanar da bullar cutar ga mutum biyu; wani mutum da ya shigo kasar daga Wuhan da ya ziyarci birnin Ho Chi Minh a farkon watan nan sa’annan ya harbi dansa da cutar.