✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ciyar da dalibai ya lakume miliyan N523 a lokacin kulle

An kashe miliyan N523 a jihohi uku wajen ciyar da dalibai a gidajensu a kullen COVID-19

Shirin ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajensu a lokacin kullen COVID-19 a Najeriya ya lakume Naira miliyan 523.3, a cewar Gwamnatin Tarayya.

Ministar Agaji da kyautata rayuwa Sadiya Farouk, ta ce an aiwatar da shirin ne a jihohi uku bayan rufe makarantu a ranar 29 ga watan Maris.

Da take magana a taron kwamitin yaki da COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin a Abuja, ministar ta ce, “Shirin ciyar da dalibai a gidajensu ba ma’aikatarmu ce kadai ta kirkiro shi ba.

“Bayan umarnin Shugaban Kasa, ma’aikatar ta tuntubi gwamnatocin jihohi ta hannun Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kafin su yi ittifaki cewa kai wa yara abinci gidajensu shi ne hanya mafi inganci na ciyar da dalibai a lokacin kullen.

“Masu ruwa da tsakin sun cimma matsaya cewa a faro shirin daga Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun a matsayin gwaji.

“Don haka shawara ce ta hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar da gwamnatocin jihohi cewa a ciyar da yaran a gidajensu.

Ministar ta kara da cewa tattaunawarsu ta kuma cimma matsaya a kan kashe N4,200 a matsayin abincin yara uku a kowane gida daya a wata.

“Alkaluma Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) sun nuna kowane gida a kasar na da kimanin yara 3”, don haka da abin ma’aikatar ta yi amfani ke nan.

Ta ce bisa tsarin shirin ciyar da dalibai na kasa, kowane dalibi zai samu abinci na N70.

A kwanaki 20 da ake zuwa makaranta a wata daya za a kashe wa kowane yaro N1,400 ke nan, jumullar abin da yara uku za su ci a wata shi ne N4,200.

“Ta haka ne muka cimma matsaya kan cewa N4,200 ne abincin dalibai a kowane gida.

“Yarjejeniyar da aka yi shi ne Gwamnatin Tarayya ce za ta samar da kudade, jihohi kuma za su samar kayan aiki”, kamar yadda ta ce.

“Domin ganin an yi komai a fili, mun yi hadin gwiwa da Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta bangare kwarewa.

“Sannan ma’aikatar ta yi aiki da hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci na da suka hada da EFCC da CCB da ICPC da DSS”, inji ta.

Bayan haka kuniyoyin kare hakki sun bibiyi yadda shirin ya gudana. “TrackaNG ta yi bibiya sannan ta rika bayar da alkaluman duk ibin da shirin ya yi a kowace rana”, inij Minista Sadiya.

Ta ce gidaje 124,589 ne suka amfana da shirin ciyarwan daga ranar 14 ga watan Afrilu zuwa 6 ga watan Yuli, 2020.

“Idan aka ba wa gidaje 124,589 abincin yara a kan N4,200, jumulla shi ne N523,273,800”, a cewarta.

Ta ce a Abuja gidaje 29,609 sun amfana, a Legas kuma 37,589 yayin da aka samu gidaje 60,391 a jihar Ogun.