✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cinikin Jariri: Masarautar Kano ta kori Mai Unguwar Fage

Masarautar Kano ta sanar da sallamar Mai Unguwar Sabon Gari, Malam Ya’u Muhammad bisa samun sa da hannu a cinikin wani jaririn da aka tsinta.…

Masarautar Kano ta sanar da sallamar Mai Unguwar Sabon Gari, Malam Ya’u Muhammad bisa samun sa da hannu a cinikin wani jaririn da aka tsinta.

Sakataren Galadiman Kano Abbas Sunusi, wato Muhammad Umar, shi ne ya sanar da warware rawanin Mai Unguwar a Kano ranar Talata.

Ya ce Majalisar Masarautar ta dauki matakin ne bayan wani bincike da Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) ya same shi da hannu a badakalar.

Rahotanni dai sun nuna tun da farko an zargi mai unguwar ne da Kwamandan Hukumar Hizbah na Karamar Hukumar Fagge, Jamilu Yusuf da hannu a ciki.