A rana ta kofar hanci ga watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, amintattun ’yan kwadagon buga amintattun jaridun kasar Haurobiya sun yi cincirindo a shigifar cucci ta zamani da ke hedkwatarsu a Haurubja, don karrama gwarazan masu laluben kadago a kamfanin Dalilin-taron su. A wurin wannan cincirindon, ni ma an tsarma ni a jerin gwarazan cin gwaza.
Da aka sanar da ni cewa, ni ma gwarzo ne a cikin gwarazamn cin gwaza, sai na rera wakar gwkarzon gwaraza a wajen cin gwaza, na kuma tuna yadda a da muke yin kama idan mun shiga yawon daji. ‘Gwarzon gwaraza a wajen cin gwaza, tuni nai gaza.’
Da mun yi kama, inda muke samun katuwar gwaza, mu tona rami mu cusata, sannan mu banka mata wuta. Bayan mun dawo daga yawon mu a gandun daji, sai mu tona ramin, don tabbatar da cewa, sanwar da muka yi a rami ta gasu. Ni dai na dade ba na yin kama, hasalima na manta da ita, ban snai ba ko mutanen kauye har yanzu suna yin wannan tsohuwar ta’addar girki a cikin rami. Oho!
Sanin kowa ne cewa, a kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya ba a yin kamar gwaza, sai dai ta manyan warkoki da kurmusun kalamai da batutuwan Haurobiyawa da daukacin al’ummar duniya. Babban dai abin da nike so a fasko shi ne, wai an ce ni ne GWARZON watan NOMAN-BABA, inda na yi watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu a jaridun Amintacciyar Haurobiyawa da kuma wadda ake murguda baki kamar ana cin kilishi, sannan a kan ga gilishi a yi ta yaren Ingilishi, wato dai ana nufin Dalilin-taron-su.
Haurobiyawa, ya kamata ku fasko cewa na zama ‘Gwarzon watan Noman-Baba ne,’ ba don na yi wa baban mu sana’ar na-duke ba; ko kuma dashen gwaza ba. A’a an dai kambama kimar daraja ta ne saboda KATAFAREN KOREN SHINGE.
Wannan cicciba kimar daraja da aka yi mini ta nusar da ni muhimmancin laluluben ‘Gararumar garka da gayauna,’ amma ban da kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Uwa-uba hada-hadar sarrafa dukiyar al’ummar duniya ana sa ran zai juya akala wajen sana’ar na-duke, don haka a daukacin nahiyoyin duniya ake ta fafutikar inganta gandun daji, ta yadda za a kare shi daga zaftarewar kasa da kwararowar rai-rai.
Lallai a wannan karon jiga-jigan jagorancin kwadagon neman kadago a kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya sun yunkura wajen tabbatar da adala, da kawar da juhala. Domin sun ce abin da ya sanya suka karrama KATAFAREN DIREBAN ALLI, shi ne, a lokacin ina fama da ‘Guguwar sauyin sawu,’ inda na rika takawa dingis-dingis, amma duk da haka na lula bisa hanya har na shiga Jihohin dakin-kara da Zaman-fara, inda na kalato muhimman bayanai kan yadda hukuma a kasar Haurobiya ke gudanar da shirin KATAFARTEN KOREN SHINGE.
A yankunan karkara da ke karkashin masarautar birnin Dikko na ga yadda ake fafutikar kare garka da gayauna daga kwararowar rai-rai, tare da shingeta daga illolin da ka iya aukuwa sanadiyyar zaftarewar kasa. Sai dai lamarin bai yi mini dadi ba, a lokacin da na nausa cikin kauyukan da ke karkashin Jihar Zaman-fara, musamman ‘Kwarin samfarera,’ inda na ga wallen hukumar da ta kasa biyan ladar kwadagon mai kula da tsirrai da kwakware mai aiki da makamashin rana. Batutuwana, wasu sun yi wa hukuma dadi, wasu kuwa an ji su bambarakwai. To kun dai ji tushen labarina. ‘Wannan shi ne labarina,’ taken wani shirin akwatin magana na Babban Bakin Ce ce- ku ce da ke birnin Lantsandan.
’Yan makaranta, musamman masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, wajibi ne mmu himmmatu ka’in da na’in wajen tallafa wa Gwamnatin Haurobiya wajen aiwatar da shirin Katafaren koren shinge,’ ta yadda za mu samar da wuraren sana’ar na-duke, wato dai garka da gayauna, inda za mu rika ribatar kayayyakin dundume kururu. Domin malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, ya furta cewa, ‘da ruwan tumbi ake janyo na kwakware.’
Sannan akwai bukatar a samar da makekiyar makiyayar fullo, inda za a killace nagge da karsana da bujimi, don samar da naman watanda da abinci mai gina jiki, don inganta garkuwar uwar jiki.
A matsayina na gwarzon gwaraza a wajen cin gwaza, kuma ‘Gwarzon watan Noman-Baba,’ ina roko Gwamnatin Baba-burin-huriyya da Usainin-Babajo su himmmatu ka’in da na’in wajen bunkasa shirin Katafaren koren shinge da sana’ar na-duke, ta yadda masu fuka-fukin tashi mutane Mista Dalung za su daina neman kwadagon farar kwala, ta yadda za su fantsama wajen farde garka da gayauna; su kuma kafa katafaren shago irin na mutanen Mao Zedong, wato Dung Fong, ni kuwa in yi kaka-gida a matsayina na Dodong, idan na samu tallafin Gwamna Lalong sai in dauki ’yan dakon kayaa cikin mutanen Mista Gizagong. Daga nan sai in cefanar da su a kasar Sin, ta hannun kamfanin safara a babban kwale-kwalen Guohang.
Zan karkarer batutuwan karramawar da aka yin mini a shigifar zamani, tare da zarata kuma gwarazan ’yan kwadago masu neman kadago da fatan kowa zai bayar da gudunmuwarsa wajen inganta shirin ‘Katafaren koren shinge, musamman al’ummar Arewacin Haurobiya. Wata rana sai kawai ku ji cewa, mun yi cincirindong da Dodong da Gizagong a Filfilon-toto cikin shigifar dashen shakushe, tare da Mista Dalung da Gwamna Lalong.
Cincirindon shigifar amintattu
A rana ta kofar hanci ga watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, amintattun ’yan kwadagon buga amintattun jaridun…