A rana ta karamin lauje da manuniyar sama ga watan A-farin lilo na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, ’yan makaranta da ke koyon watsattsake da buda wagagen litattafai a wannan farfajiya, sun yi gagarumin gangamin dodanni a gusun da birnin Shehu, inda aka gabatar da batutuwa kan yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba; an kuma yi batuuwa kan yadda harshe ke kasura da tumbatsa a sararin duniya.
Jihar Zaman-fara ko Mu-muka-fara shari’a, a babban birnin Gusun, ’yan makaranta sun yi baki kyakkyawar tarba, inda suka tanadi kayan dundume kururu samfurin kirar Zaman-fara, wato abin suke yi wa lakabi da Hoce. Sannan sun sauke Malam Dodo da tawagar jiga-jigan kungiyar dalibai a masaukin al’umma na “Godiya,” da ke kan titin zuwa akurkin tsohon Gwamna Gwaramgwam Mai shinkafa.
A wajen wannan cincirindo na dodanni da aka gudanar a birnin Gusun, Malam Na Gidan dan iccen Buda-baki, ya gabatar da makala kan tumbasa da kasurar yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba, inda ya yi tsokaci kan alakar kafofin sadarwa, musamman shafukan mashakatar lilo da tsallake-tsallake da yaduwar harsh a ko’ina cikin sararin duniya. Ya yi batutuwa kan akwatunan Magana da muke da su a kasashen duniya, wadannan suka hada da Babban Bakin Ce ce ku ce na birnin Lantsandan da Muryar kasar Uban-mama da Jama’ar Jamusawa. Uwa-uba ya karkare batuuwansa, inda ya tabbbatar wa mahalarta cincirindon dodanni cewa taron Dodorido na kasar Haurobiya ma wata alama ce da ke nuni da kasura da tumbatsar Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba. Daga bisani ya yi tufka da warwara, bayan ya lasa mana zuma, sai kuma ya dandana mana madaci, inda ya bijiro da barazanar da masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai ke fuskanta. Don a kalallamun kalamansa, ya furta cewa “a rasa dimbin jiga-jiga al’umma a jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya da na kasashen ketare, musamman wadanda su ci farfesun ilimi a yaren Hau-hau. Kuma babu wani namijin motsi da ake yi cike guraben da wadannan kwararru suka bari.”
Malam Ahmadu dan Hashimu, ya yi godiya ga daukacin mahalarta cincirrindon dodanni a Gusun, sannan ya gabatar da direban alli da daukacin gunduma-gunduma baki. Don haka aka tayar da ni, don in kwaroro wa ’yan makaranta bayanai kan yadda aka samu tushen kafuwar Farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a amintatar jaridar kasar Haurobiya. Ni kuwa na tashi na yi ta zuba kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, mai rututun labarai, inda na dauko batu kan yadda na kawo wa Shugabar Amintatar jaridar kasar Haurobiya ta farin farawa shawarar bullo da shafin Dodorido a shekara ta dubu karamin lauje da manuniyar sama; ita kuwa ta amince, na kuma samu goyon bayan abokan kwadagona.
Dan a dan sahirta da batutuwa na kan tushen kafuwar Dodorido, sai Hajjaju Makkata Nana ta gidan Akwatin Maganar Zamanfara ta roke ni kan lallai in yi mata faskaren ma’anoni. Wani mai rera wakoki shi ma ya bijiro da tambaya kan ko su mawaka za su iya kawo dauki a wajen gudanar da darussan makaranta. Shi ma Na gidan dan Iccen Buda-baki ya taimaka wajen yi mini rubdugu da tarin tambayoyi, inda ya bukaci in bayyana masa yadda nasan cewa ana fasko manufofin darussan makaranta; ko mun taba afkawa cikin rikici; sannan wane tasiri muka taba yi wajen warware matsalolin Haurobiya?
Ganin cewa mafi yawan wadanda suka halarci cincirindon dodanni a Gusun duk sun kakaba wa kawunansu tagiyar Malam Tambaya, sai kawai na yi kikam, na fara faskaren ma’anoni, tare da bijiro da gamsassun amsoshi. Na fara da Hajjaju Makkata ta Gidan Akwatin maganar Zaman-fara, inda na nusar da ita yadda ake zube alkaluman kididdiga tun daga kan sili zuwa sili da zagaye. Mai waka kuwa, na rera masa baitukan sananniyar wakarmu ta “Calka ko wahanda. Malam Ya handame kaza. Har zuwa Kaiku ta shi mu tafi UGANDA! Asalin calka ko wahanda dai wani malaminmu ne ya handame kaza, ya bar mu a busasshiyar doya, don haka muka nusar da shi rashin alfanun kiwon dan tsako! Kuma mu malaminmu ai ya yi gyara, sai dai muna fatan bai yi ’yan yare-gyare irin gyare da kurege ba.
Shi kuwa na gidan dan Iccen Buda-baki, sai na bijiro masa da karon batar mu da tsohon Magajin garin Harubja Babban birnin Haurobiya, bayan da na yi masa darasi mai taken “’Yar Landan a hannun Zaratan Zambiya.” Na kuma ba shi labarin yadda na ziyarci gari mai kama da sunan Kububuwa a cikin zungureriyar shoridon Malam Nasara el-Rusau, har na hadu da wata mai wa’azin addu’a da giciye da ta yi artabu da wani mutum da rika jin ta dame shi da batutuwa. Abin da kuma ya biyo baya, hukumar wannan birni ta bayar da sanarwar duk wanda ya shiga cikin shorido to ya ja bakinsa ya tsuke kada ya addabi mahayan shorido da zantuttukan da ba a tambaye shi ba.
Malam Na gidan dan Iccen Buda-baki ya nuna gamsuwar kan cewa lallai ’yan makarantar Jihar Zaman-fara, wato Mu-muka-fara Shari’a sun yi rawar gani.
kungiyar Masu shirin majigi, sun shirya wasan koyi-ka-koyar kan muhimmancin halartarFarfajiyar Koyon Wtsattsake da buda wagagen littattafai ta Dodirido da ke cikin amintattar Jaridar kasar Haurobiya. Sun kuma rera wakar yabon ‘Hoce’ kayan dundume kururun Zaman-fara, inda suka yi wa mutanen Jihar Tumbin-giwa shagube. Ni dai na ji suna rerawa: Hocenmu na Zaman-fara, ya zarta gurasa ta Kanawa.” Duk da cewa wakilan jihohin Yawon-Bebe da na bayan-Kada sun nemi uzuri saboda wasu sabgogi da suka sha musu gaba, hakika cincirindon dodanni a birnin Gusun ya kayatar!
Cincirindon Gusun
A rana ta karamin lauje da manuniyar sama ga watan A-farin lilo na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya,…