✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka

Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka   Cincirindo ’Yan kwadago dodo-dodo Hargowa da harigido Tsibin kayan dadi a Kwando Wani abincin yai kama da bado   Kamfanin Dalilin-taronsu…

Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka

 

Cincirindo

’Yan kwadago dodo-dodo

Hargowa da harigido

Tsibin kayan dadi a Kwando

Wani abincin yai kama da bado

 

Kamfanin Dalilin-taronsu

Kun hadu da masu tafka musu

Labarin kuliya da kusu

Kowa ya diro a kansu

Ban da shahasha da sususu

 

Baffan Editoci

Ya nuna karamci

Muma kada mu yi butulci

Ko zantukan batanci

Sai mu dan yi kawaici

 

Zancen ba habaici

Masu jefa mu cikin kunci

Da ke nuna bambanci

Ina tai muku barkwanci

Har an dauke ni dillalin dolanci

 

Jita-jitar jakkanci

Sakatar subul da bakan sokwanci

Dabarbarun dabbanci

korafi da kulafuci

Tubulin tada ginin Turanci

 

Dokoki na bukatar kanikanci

Don kawar da jahilci

Sai a tabbatar da adalci

Kowa da kowa a samu kusanci

Sai mu kauce wa kaskanci

 

’Yan gada-gada

Sun yi kaka gida

Suna ta baragada

Sun gaza haura gada

Mu dai dare kan danda

 

A kiyayi far-far-da-ganda

Kar a kwada muku sanda

Farmaki miyagu har su saduda

Mu rage yawan kasada

A daina waskiya a fada

 

Ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka

Ciranin kaka

Cari da caccaka

Cizon cinnaka

Cankar kubu da caka

 

Gwarzon gwaraza

Gutsuri gwaza

Gafalallu sai an gwabza

Girrgiza-girrgiza

Gundumi ya gaza

 

A tabbatar da adala

A kawar da juhala

Doka na hana wahala

Mai laifi a tsala masa bulala

Sila ta fi salsala da salala

 

Ga karatu dalla-dalla

Watsatsaken kauce wa cin kwala

Wasu na ta cin alala

Sun samu salala

Sun bar mu muna lalalala

 

Wa’adin sallama

An samu makama

Malam da malama

An bi ku da lalama

Yanzu a nai muku takama

 

Kar ai mana cin duhu

An nunke mu a buhu

Nauyinmu huhun ma’ahu

Ba a saye taro da ahu

A daidaita sahu

 

kiren karairayi

Ciwonsu na da kaikaiyi

Ciniki babu tayi

A sai kayan yayi

A kauce wa dibar yayi

 

Masu mukami

Kun dau makami

Kuna yi mana bambami

Kar ku jefa jama’a zullumi

A karke da salallami

 

Fanco

Watsattsaken kan ga gilashi

Murguda bakin cin kilishi

Cikin harshen ingilishi

Kaico!

 

Gadin yana

Gudun magana

Garadan gidan zana

Gardamar masana

Gada-gadargarada na zayyana

 

Burgar bugun gadi

Banga-da-gadi

Bugar gardi

Baragada marar adadi

barambaramar kaidi

 

A kiyayi surutun ’yan baka

Otal din Ci-da-kanka

An nemi a kyautata ayyuka

Kiraye-kirayen shugabanni duka

Wasu sun ci kare ba babbaka

 

Kwankwatsa da tsattsagar ci-maka

dundume kururu da marka- marka

A dubi na-mujiyar hankaka

Mayar da dan wani naka

Zalunci ke haifar da kiki-kaka

 

Ja-gaban masu watsattsake

Wassafa tsarin damo-da-kura-diyya

Wasan Samson siya-siya

’Yan takara na take-take

Masu taka-kara na make-make

 

Malam Mahmudu

Yai awo a mudu

Siyasa an tafka rudu

Neman mukami har a Bungudu

Sun karade Arewa da Kudu

 

A rana ta karamin lauje da sili ga watan Ukun-toton-Baba mun halarci CINCIRRINDON CE-CE-KU-CEN CI-DA-KANKA, inda muka kwashi kwalamn da makwalashe, a wajen tande-tande da lashe-lashe, muka yi nashe-nashe. Kodayake dai da farin farawa Baffan Editocin kamfanin wallafa Amintattun jaridun kasar Haurobiya ya bijiro da batutuwa kan yadda za a inganta watsatttsaken rahotannin al’amuran da ke wakana a daukacin fadin Haurobiya. Sai kuma malam Mahmudu Ja-gaban masu watsattsake a jaridar Dalilin-taronsu, wanda ya nusar da mu yadda ake lalubo batutuwan masu wasan Samson siya-siya da kwakwalen talakawa don neman darewa bisa karagar mulki.

Su ma jiga-jigan jan ragamar ’yan kwadagon wannan kamfani sun bijiro da baturtuwansu, inda suka karke da mayar da martini korafe-korafen ’yan kwadagon kamfanin da ke ganin akwai NAdI A CIKIN LAUJE game da sababbin  tsare-tsaren da aka fito da su, musammman kan wadanda ke hankoron RIRITA TAYA ko MURABUS daga fafutikar cin CUKUBUS da ALGARAGIS da ALKUBUS kafin su rrankaya birnin TAGADAS wajen CACUMAR masu CAMMMAR cin CA’AMMAS, don sauke nauyin kayan da aka jibga musu, inda suke ta artabu da KULIYA DA KUSU, wadanda ke kyarar baza labarin yadda suka bula ASUSU, suka mayar da al’ummar kasa taron SHASHASHA DA SUSUSU.

Batu na ingarrman karfen karafan titin tarragon layin dogo, mun yaba kokarin kamfanin wallafa Amintattun jaridu da mujallun kasar Haurobiya, illa dai kawai akwai ’yan ba ni na iya a jerin masu jan ragamar jigata ’yan kwadago da ke haifar da tarnaki a wajen CANAKAR KUBU- JA-DA-BAkA DA CAKA na GWARZON GWARAZA a wajen cin gwaza, shi ya sa aka yi musu gunji da GAZA. Lallai a daina wasan KARTA da rayuwar ’yan kwadago masu laluben kadago a daukacin lokutan wulwulawar AGOGO. A dai tausaya wa su GWAGGO. Kuma akwai ’yan dugwi-dugwi da ke gararamba a KANGO ja-gabansu shi ne GIZAGO, uhm! Giza-gizon dakin GWAGGO. Wasu na shirin samun gwaggwabar ladar kWADAGO. Idan kuwa ka ga na-mujiya kURU-kURU, to an samu masu SHARbAR SHAWARMAR SHIRRUWA SHIRU, da sun ci sun tande sais u bar kowa ya yi ZURU-ZURU.

Su kuwa ’yan makaranta masu koyon watsattsake da fallee shafukan mujallu da makalu a Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya sun yi DODO-DODO karkashin jagoran Malam DODO na farfajiyar DODORIDO, wanda ke fafutikar ganin an hana kWADO da darar HARIGIDO da rayuwar al’umma dungurugum. Don haka na yi ZUGUM zan yi GUM. Kada a bari ‘ya’yan innna da baba su yi DUKUM! Kunkumadi launin KUM-KUM!

Haurobiyawa a bi  kA’IDA don samun FA’IDA, sannan a bi DOKA don kada kowa ya KOKA! Sai a kiyayi shaci-fadin ’yan BAKA rrani da KAKA!

Wannan shi ne Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka da kamfanin wallafa jariodu da mujallu ya saba gudanarwa a kowace shekara, don kada a yi kakara a wajen taka-kara ko neman mukami a wajen takara. Mun dai samu sarrafa SAMFARERA daga ribar SAFARA, saura mu kwashi GAGARUMAR GARARUMAR GARA, in an kauce wa tsikarar na-mujiya a wajen gyaran GIRA, musamman in aka fatattaki masu tsuwurwurta ’YAN GYARE-GYARE IRIN NA GYARE DA KUREGE.

Da zarar an amsa kiran makaranta to za a daina YASAR TANKIN YUYUYU, mu kuwa mu yi ta kwankwadar NONON YUYUYU. Sai a hanzarta a tabbatar da cewa ba a yi mana FANCO ballanta mu ce KAICO!