✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin hanci ba zai bari Najeriya ta ci gaba ba — Ganduje

Babu yadda za a yi Najeriya ta ci gaba da irin cin hanci da rashawar da ake fama da su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ce babu wani ci gaba da Najeriya za ta yi madamar ba a kawo karshen cin hanci da rashawar da suka dabaibaye kasar nan ba.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da wani kwamitin yaki da rashawa a jihar Kano mai dauke da mutum takwas kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

A cewarsa, babu yadda za a yi Najeriya ta taka wani mataki na ci gaba da irin cin hanci da rashawar da ake fama da su a kasar nan.

Ganduje ya jaddada bukatar dukkan masu ruwa da tsaki da su yi duk wata mai yiwuwa wajen kawo karshen cin hanci da rashawa a jihar Kano.

Ya ce, “za ku yarda cewa cin hanci yana kashe mu a kasar nan, don maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci, kuma ba za mu motsa ko ina ba,” in ji Ganduje.

Ganduje wanda sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya wakilta, ya ce an kaddamar da kwamitin ne da zummar rage cin hanci da kuma tabbatar da an gudanar da al’amura a bude a fadin jihar.