Zauren Majalisar Gwamnonin Najeriya (NGF), ta sanar da shirinta na fara aiwatar da dokar cin-gashin-kai ta hukumomin shari’a da kuma majalisun dokoki.
Shugaban sashen hulda da jama’a na Zauren Majalisar Gwamnonin, Abdulrazaque Bello-Barkindo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Sanata Goje ne ya fi dacewa da Shugabancin APC — Kungiyoyin matasa
- Kungiya ta bukaci a soke Hukumomin zaben jihohi
Ya ce gwamnonin za su tattauna kan ‘Yarjejeniyar Aiwatarwa’ da suka sanya hannu a kai tsakaninsu da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a da ta Majalisar Tarayya.
A cewarsa, tabbatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki shi zai sa kungiyoyin kawo karshen yajin aikin da suka shiga a kwanan nan.
Sanarwar ta ce, “A dukkanin jihohin kasar nan, ana nan ana ta kokarin ko dai kafa Kwamitocin Asusun Tara Kudaden Jihohin (SAAC) ko kuma kaddamar da su domin fara aiki a shirin da ake yi na bai wa bangarorin gwamnatin cikakken ikon cin gashin kansu a matakan jihohin.
“Kungiyoyin biyu — JUSUN da PASAN — sun yi yajin aikin fiye da wata biyu, yayin da gwamnonin 36 ke karakainar yadda za a samar wa ma’aikatan cikakken ikon cin-gashin-kansu daidai da tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan.’’
Ko da yake ya ce taron gwamnonin zai kasance dan takaitacce kafin su tattauna kan batun yarjejeniyar aiwatar da batun ’yancin cin gashin kan.