✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chukwu Eze Romeo da Salihu Makera da AbdurRahman A. Dodo

Bayan gundarin kasa da muke taka wa, muke rayuwa a kai, muke gine-ginenmu da shuke-shuke don samun abinci da rayuwa, bangare mafi girma da Allah…

Bayan gundarin kasa da muke taka wa, muke rayuwa a kai, muke gine-ginenmu da shuke-shuke don samun abinci da rayuwa, bangare mafi girma da Allah Ya halitta wa dan Adam don gundanar da rayuwarsa a wannan duniya shi ne tekunan dake gewaye da ilahirin gundarin kasar da muke kunshe a ciki. Wannan bangare kuwa shi ne tekuna (manya da kanana) da rafuka da gulabe da sauran mabubbugan ruwa wadanda dan Adam bai da hannu wajen samar da su, balle abubuwan dake cikinsu. Wannan bangare na duniya yana da tasiri matuka ga rayuwarmu a bangaren abinci, da kasuwanci, da al’adu, da addini da sauransu. Kowace al’umma tana da wani matsayi na musamman da take baiwa tekunan dake gewaye da wannan duniya tamu; ko dai a al’adance ko kuma a addinance. Ba wannan ba kadai, malaman kimiyya sun yi ninkaya wajen kokarin gano taskokin dake ciki da karkashin wadannan tekuna na duniya, har yanzu dai ana kai. Abubuwan da suka gano, kadan ne cikin kadan na abubuwan da ba su gano ba.

Kamar yadda na yi alkawari a makonnin baya, a yau za mu juya akalar bincikenmu ne zuwa kan tekunan duniya baki dayansu. Duk da cewa a baya mun yi nazari har sau biyu a wasu bangarorin da suka shafi teku – a karon farko mun taba bayani ne a doguwar kasidarmu mai take: “Kimiyyar kur’ani da ta Zamani – A Ina Aka Hadu?”, a karo na biyu kuma mun taba bayani kan teku a takaice, cikin kasidarmu mai tsawo ita ma har wa yau, mai take: “Ruwa da Nau’ukan Sinadaran dake Cikinsa.” Wannan karo bincike zai ta’allaka ne kai tsaye kuma kacokam, kan Tekunan Duniya (World Oceans), da yadda suka samu, da yanayin girmansu, da karkasuwarsu, da abubuwan da suke dauke da su na halittu da abinci, da kuma tasirinsu wajen rayuwar dan Adam a bangaren tattalin arzikin kasa, musamman. A halin yanzu ga bayani kan hakikanin teku, da siffofin da suka kebance shi:

Teku… Teku… Teku…
Kalmar “Teku” ko “Ocean” a harshen Turanci, na ishara ne ga wani bangare na jimillar tarin ruwa da Allah Ya samar a duniya baki daya. A wani kaulin kuma, Malaman kimiyyar teku (Oceanographers) sun ce: Teku wani bangare ne daga cikin bangarorin duniya masu dauke da ruwan gishiri da suka kunshi kashi biyu bisa uku (2/3) na fadin wannan duniya tamu. Manyan bangarorin dake dauke da mafi girman kaso na ruwan gishiri dai su ne: Tekun Pacific (Pacific Oean), da Tekun Atilantika (Atlantic Ocean), da Tekun Indiya (Indian Ocean), da Tekun Kudancin Duniya (Arctic Southern Ocean), da kuma Tekun Aktik (Arctic Ocean). Wadannan tekuna kowannensu yana da bigirensa na musamman, kamar yadda mai karatu zai gani nan gaba.
Kamar yadda suka karkasu ta fuskar bigiren da kowannensu yake, haka kuma tekunan duniya sun karkasu wajen girma. Akwai manya. Akwai matsakaita. Sannan akwai kanana. A turancin zamanin yau, idan aka ce: “Ocean” ana nufin daya ne daga cikin manyan tekunan duniyan nan guda biyar da na zayyana su a sama. Amma idan ka ga kalmar “Sea,” to ana nufin karamin teku kenan. Kamar irin su “Capsian Sea,” da “Red Sea” da sauransu. Wannan a bangaren ilimin kimiyya kenan a zamanin yau. Amma a tsagwaron harshen turanci, babu wani bambanci tsakanin kalmar “Ocean” da kalmar “Sea.” Kalmar “Ocean” harshen turanci ne, amma lahajar mutanen kasar Amurka ce, kuma tana nufin teku ne. Ita kuma kalmar “Sea” harshen turanci ce amma lahajar mutanen kasar Ingila ce, ita ma tana nufin teku ne. A karshe dai, masana sun tantance lamarin. Inda suka tabbatar da kalmar “Ocean” wajen nufin “Babban teku, ko kuma daya daga cikin manyan tekunan duniya da sunayensu suka gabata.” Ita kuma kalmar “Sea” aka tabbatar da ita wajen nufin “Matsakaici ko karamin teku.” Duk da haka, har yanzu akwai wadanda ke amfani da kalmar “Sea” wajen nufin daya daga cikin manyan tekunan duniya.
Ruwan Tekunan Duniya
Kamar yadda mai karatu ya karanta a sama, tekunan duniya suna dauke ne da ruwa mai dandanon gishiri. Wannan shi ne malaman kimiyyar teku ke kira “Saline Water.” A daya bangaren kuma, ruwan gardi, wanda muke iya sha shi suke kira “Fresh Water.” dandanon ruwan teku dandano ne irin na gishiri. Ba ya shayuwa ta dadi. Yana dauke ne da sinadarin ayon (iron), wanda malaman kimiyya suka ce bai dace da jikin masu ciwon hauhawan jini ba. Shi ya sa idan ka je kasashe irin su Saudiyya misali, inda galibin ruwan da suke amfani da su wajen aikace-aikace ruwan teku ne da aka tace, za ka ga sun rubuta sanarwa cewa: “Wannan ruwa bai dace a sha shi ba, saboda sinadaran dake dauke cikinsa suna da yawa.” Wannan tunatarwa ce mai fa’ida, don lafiyar mai mu’amala da ruwan. Sai dai a yi wanki da shi, tare da cewa sun yi iya kokarinsu wajen tace shi kenan, da rage masa karfi ta yadda mu’amala da shi wajen tafiyar da harkokin yau da kullum zai saukaka.
Kashi 72 na fuskar wannan duniya tamu na dauke ne da ruwan gishiri. Wannan ruwan gishiri shi ne ya karkasu zuwa bangare-bangare, abin da a yanzu muke kira teku; manya (Oceans) da kanana (Seas). Shi ya sa wasu malaman kimiyyar teku suke cewa, asalin tekunan da ke duniya teku ne guda daya tak. Abin da ya raba tsakaninsa kawai shi ne bigirorin duniya; Gabas ne, ko Yamma, ko Kudu, ko Arewa. Domin asalinsa daya ne. dandanonsa daya ne. Da bigire da zurfi ne kawai suka rarraba shi. Idan aka tara dukkan ruwan dake wannan duniya tamu, kashi 97 daga teku ne. Sauran kashi 3 ne kadai ke samuwa daga ruwan sama ko gulabu da rafukan dake tsakanin tudun kasar da muke rayuwa a kai.
Malaman kimiyyar teku (Oceanographers) sun tabbatar da cewa tekunan duniyar nan gaba dayansu wata taska ce Allah Ya ajiye abubuwa da dama don maslahar dan Adam. Ta bangaren ruwan dake cikinsu, suka ce yawansa ya kai biliyan daya da miliyan dari uku a ma’aunin “cubic kilometre” (1.3 billion cubic kilometre). Makurar zurfinsu kuma ya kai mita dubu uku da dari shida da tamanin da biyu (3,682 meters), wanda yay i daidai da taku dubu goma sha biyu da tamanin (12,080 feet). Sun sake tabbatar da cewa tekunan duniyan nan suna tasiri matuka wajen sauyawar yanayi (Seasonal and Weather Changes), tsakanin zafi, da sanyi, da iska, da raba, da danshin dake samuwa a mahallinmu.
Ta bangaren halittun dake cikinsu, malaman kimiyyar teku sun gano cewa tekunan duniya (tsakanin manya da kanana) suna dauke ne da na’ukan halittu da adadinsu ya kai dubu dari biyu da talatin (230,000 life species). Kuma har zuwa yau da ake ta bincike, suka ce ba su samu kaiwa karkashin wadannan tekuna ba. Dangane da asali kuma, malaman kimiyyar teku sun hadu kan cewa (a iya bincikensu), babu wanda ya san hakikanin asalin wadannan tekuna dake duniya har yanzu. A karshe sun tabbatar da cewa, duk da tarin abin da suka gano na ilimi wanda ake ta karantar da dalibai a jami’o’i da tarin binciken da suke ta yi a kullum (daga na malaman jami’a zuwa na cibiyoyin ilimi da na hukumomin gwamnatoci) har yanzu abin da aka gano na ilimi dangane da tekunan duniya bai wuce kashi 5 ba cikin 100. Haka ma wuraren da aka taba shiga ko gani daga cikin tekunan duniya, duk ba su shige kashi 5 ba cikin 100. Wannan ke nuna mana girma da kudurar Ubangiji wajen halitta, a bangare daya. A daya bangaren kuma, yana nuna mana matukar rauni da gazawar dan Adam wajen iya tantance hakikanin girma da fadin ni’imar Ubangiji ga bayinsa.
Kalmar Teku a Al-kur’ani
Masana harshe suna cewa, yawan ambaton abu na nuna matukar mahimmancinsa ne. Dangane da haka, a cikin Al-kur’ani mai girma Allah Ya ambaci kalmar “Al-bahar” da “Al-bihaar” da kuma “Abhurin,” a wurare daban-daban. Malamai masu tantance kalmomin kur’ani sun tabbatar da cewa Allah Ya maimaita kalmar “Al-bahar” sau 32, a cikin ayoyi 31 na Al-kur’ani mai girma. Sannan ya ambaci kalmar “Abhurin” a wuri daya. Sai kalmar “Al-bihaar” a wurare biyu. Wannan ke nuna himmar da Al-kur’ani yake bai wa wannan ni’ima da Allah Ya mana, da kokarin jawo hankulanmu don fahimtar hakan, ko kuma fahimtar misalin da Allah ke mana dangane da abin da ake kokarin jawo hankulanmu a kansa.
A wurare bakwai cikin kur’ani Allah Ya ambaci kalmar “Al-bahar” bayan ambaton kalmar “Al-barr,” wanda shi ne akasin kalmar. Wuri na farko da na biyu da na uku na suratul An-Aam, aya ta 59 da aya ta 63, da kuma aya ta 97. Wuri na hudu a Suratu Yoonus, aya ta 22. Wuri na biyar a Suratul Israa’i, aya ta 70. Sai wuri na shida a Suratun Namli, aya ta 63. Wuri na karshe kuma na Suratur Room, aya ta 41.
Sauran wuraren da Allah Ya amabaci kalmar teku kuma ya ambace su ne ba tare da gwama su da kalmar “Tudun kasa” ba, wato “Al-Barr.” Wadannan wurare kuma su ne: Suratul Bakara wurare biyu; aya ta 50 da 164. Sai Suratul Maa’ida, aya ta 96. Sai Suratul A’raaf, aya ta 138, da aya ta 163. Wasu surorin sun hada da Suratu Yoonus, aya ta 90. Da Suratu Ibrahim, aya ta 32. Da Suratun Nahl aya ta 14. kari a kan wadannan akwai Suratul Israa’i aya ta 66. Da Suratul Kahfi aya ta 61, da aya ta 63, da aya ta 79 da kuma aya ta 109.
A cikin Suratu Taaha ma an ambaci kalmar a aya ta 77. Sai Suratul Hajj aya ta 65. Da Suratush Shu’araa’i aya ta 63. A cikin Suratu Lukman aya ta 27. Idan muka gangara Suratush Shoora aya ta 32 an ambaci kalmar, sai aya ta 24 dake Suratud Dukhaan. Sauran surorin su ne: Suratul Jaathiyah, aya ta 12. Sai Suratu Toor aya ta 6. Sai sura ta karshe mai suna Suratur Rahmaan, aya ta 24. Kalmar “Al-bihaar” dake nufin jam’in teku kuma an ambace ta ne a surori guda biyu; Suratul Takweer aya ta 6, da Suratul Infitaar, aya ta 3. Kalmar “Abhurin” kuma an ambace ta a Suratul Lukman aya ta 31.; cikon kalmar dake ayar kenan.
Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai fahimci mahimmancin da tekunan duniya ke da shi kan rayuwarsa. A makon gobe za mu ci gaba da bayani kan launin teku, da sauran abubuwan da suka dangance shi. A ci gaba da kasancewa tare damu.