✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

China za ta ‘kwace’ filin jirgin saman Uganda saboda bashin $207m

Matakin nazuwa ne bayan kasar ta gaza biyan bashin da ta ciyo da Chinan.

Akwai yiwuwar bankin Exim na kasar China ya karbe iko da filin jirgin saman kasa da kasa na Entebbe da ke kasar Uganda da ma wasu kadarori saboda gaza biyan bashin da yake bin ta.

Matakin na zuwa ne duk da tawagar da Shugaban Kasar ta Uganda, Yowere Moseveni ya aike zuwa birnin Beijin na China don tattaunawa da gwamnatin kasar a kan bashin.

A watan Nuwamban shekarar 2015 ne dai gwamnatin Shugaba Museveni ta rattaba hannu a wata yarjejeniya da bankin na Exim kan bashin Dalar Amurka miliyan 207.

An shirya kwashe shekara 20 dai ana biyan bashin, ciki har da rangwamen shekara bakwai, amma yanzu alamu na nuni da cewa dole sai dai kasar ta sallama filin jirgin wanda shi ne mafi muhimmanci a kasar ga China.

Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Uganda (UCAA) dai ta ce akwai yarjejeniyar da aka cimma kan karbe iko da kadarorin, har sai an cimma matsaya a nan gaba.

A cewar jaridar Daily Monitor, tun da farko dai kasar ce ta bayar da kofar da China za ta iya kwace filin matukar ta gaza biyan bashin.

Sai dai a watan Maris din 2021, Uganda ta aike da wata tawaga zuwa China don tattauna yiwuwar yin sassauci a yarjejeniyar bashin, amma suka dawo ba tare da samun nasara ba.

Filin jirgin saman na Entebbe shi ne kadai filin kasa da kasa da Uganda ta mallaka, kuma ya kan karbi bakuncin fasinjoji miliyan 1.9 duk shekara.

Ana dai ganin matakin na China a matsayin wani muhimmin koma baya ga Shugaba Museveni mai kimanain shekara 77 a duniya.