Kasar China na shirin tsawaita atisayen soji da take yi a kasar Taiwan da ta mamaye a daidai lokacin da Kakakin Majalisar Dokokin Amurka, Nancy Pelosi ke ziyarar aiki a kasar.
Pelosi dai ta fara ziyarar ce yankin Taipei lamarin da bai yi wa Beijing dadi ba.
- Yunwa ba za ta sa mu janye yajin aiki ba — ASUU
- Najeriya ta fi kowace kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya – UNICEF
Atisayen yini shida da China din ta fara a Talatar da ta gabata bayan da Pelosi ta isa tsibirin, ya kunshi amfani da jiragen yaki samfurin J-20 da kuma gwajin makamai masu linzami.
Kamfanin Dillancin Labaran China ja Xinhua ya ruwaito cewa, ita ma Rundunar ’Yantar da Jama’a ta kasar (PLA) za ta gudanar da atisayen soji daga ranar hudu zuwa bakwai ga Agusta a wurare daban-daban guda shida a yankin tsibirin.
Sai dai Taiwan ta fada a ranar Laraba cewar, mamaye mata wuri da aka yi wajen gudanar da atisayen ya saba wa ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ta ce ka iya sanya ta rufe sararin samaniyarta da kuma tashoshin ruwanta.
A hannu gudabkuma, Pelosi ta zama Kakakin Majalisar Amurka ta farko da ta ziyarci Taiwan cikin shekara 25.
Sai dai kuma China ta yi barzanar za ta dauki mataki mara dadi dangane da ziyarar Pelosi a kasar da China ke ikirarin tsibirinta ne.