Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta nada Graham Potter a matsayin sabon Kocinta don ya maye gurbin Thomas Tuchel, wanda kungiyar ta kore a ranar Laraba.
A yanzu haka dai Chelsea ta sanar da nadin Graham kan kwantiragin shekara biyar bayan da ta amince da kudi da Brighton na sakin shi daga kwantiraginsa a filin wasa na Amex.
- An kama shi kan zargin yin luwadi da kananan yara
- Sojoji sun kama mai tattara wa Boko Haram bayanai a tsakiyar Abuja
Potter ya ce, “Ina matukar alfahari da farin cikin wakilcin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, wannan kyakkyawar kungiyar kwallon kafa ce.
“Na yi matukar farin ciki da yin hadin gwiwa tare da sabon rukunin mallakar Chelsea kuma ina fatan haduwa da aiki tare da rukunin ‘yan wasa masu ban sha’awa don habaka kungiyar wadanda magoya bayanmu masu ban mamaki za su yi alfahari da su.
“Ina kuma mika godiya ta ga Brighton da kuma Hove Albion da suka ba ni wannan damar musamman Tony Bloom da dukkan ’yan wasa da ma’aikata da magoya bayana saboda ci gaba da goyon bayan da suke yi a lokacin da nake kulob din.”
Shi kuwa shugaban kungiyar, Todd Boehly ya ce, “Mun yi farin ciki da kawo Graham zuwa Chelsea. Shi kwararren koci ne kuma mai kirkire-kirkire a gasar Premier wanda ya dace da ra’ayinmu game da kulob din.
“Ba wai kawai yana da hazaka a filin wasa ba, yana da kwarewa wanda ya wuce a filin wasa wanda zai sa Chelsea ta zama kulob mai samun nasara.