✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta nemi Madrid ta biya Naira biliyan 47 a kan Hazard

A ranar Talatar da ta gabata ce kafofin watsa labarai suka ruwaito yadda kulob din Chelsea da ke Ingila ya sanya farashin Fam miliyan 100 (kimanin…

A ranar Talatar da ta gabata ce kafofin watsa labarai suka ruwaito yadda kulob din Chelsea da ke Ingila ya sanya farashin Fam miliyan 100 (kimanin Naira biliyan 47) ga dan wasan gabansa Eden Hazard ga duk mai bukatar sayensa, musamman kulob din Real Madrid da ke Sifen.

Eden Hazard wanda saura kimanin wata 18 kwantaraginsa ya kare a kulob din Chelsea, ya nuna sha’awar komawa kulob din Madrid a karshen kakar wasa ta bana.

Jaridar The Mirror ta Ingila ta kalato cewa, mahukunta kulob din Chelsea sun sanar da Madrid cewa muddin suna son Hazard to sai sun ajiye Fam miliyan 100.

Kulob din Madrid dai ya taba sayen Gareth Bale a kan Fam miliyan 87.5 (kimanin Naira biliyan 42 da miliyan 212) a shekarar 2013 kuma a tarihi shi ne dan kwallon da ya fi tsada a kulob din. Sai dai masana harkar kwallo suna ganin da wuya in kulob din zai iya sayen Eden Hazard a kan wannan makudan kudi.

Tun a bara Hazard ya so komawa Madrid amma koci Maurizio Sarri ya lallashe shi inda ya ci gaba da yi wa kulob din Chelsea kwallo a bana.

Eden Hazard mai shekara 28, hakan ya nuna shekaru sun fara  yi masa nisa a harkar kwallo.