A ci gaba da Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League), a wasannin da aka yi a daren Talata, Chelsea ta samu nasara a kan Lille da ci biyu da nema, yayin da Villarreal da Juventus suka yi canjaras.
Chelsea ve dai ta karbi bakuncin Lille a filin wasa na Stamford Bridge da ke birnin Landan.
- Rikicin Ukraine: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya
- Matashin da ake zargi da tattaka Kur’ani ya sha da kyar a Kano
Dan wasan gaban Chelsea Kai Havartz ne ya fara jefa kwallo a minti na takwas da fara wasa.
A minti na 63 uku kuma, Christian Pulisic ya ci wa Chelsea kwallo ta biyu.
Sai dai kocin Chelsea, Tomas Tuchel, bai yi amfani da Romelu Lukaku ba saboda rashin bajinta da yake yi.
A daya wasan kuwa, Villarreal ce ta karbi bakuncin Juventus a filin wasa na De la Ceramica, a kasar Spain.
Juventus ce ta fara jefa kwallo a minti farko na wasan, ta hannun sabon dan wasan gabanta, Dusan Vlahoci.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, dan wasan Villarreal Daniel Parejo ya farke cin a minti na 66.
A ranar 16 ga watan Maris za a dawo gasar don ci gaba tare da fitar da kungiyoyin da za su je matakin quater final.