✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta karkata akalarta a kan Aubameyang

Kulob din Chelsea da ke Ingila yanzu ya karkata akalarsa ne zuwa dan kwallon gaba a kulob din Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang don ganin ya…

Kulob din Chelsea da ke Ingila yanzu ya karkata akalarsa ne zuwa dan kwallon gaba a kulob din Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang don ganin ya dauke shi bayan ya rasa dan kwallon Everton Romelu Lukaku.


Sai dai rahotanni sun nuna kulob din zai fuskanci qalubale a wajen kulob din PSG na Faransa da kuma na Real Madrid da ke Sifen wajen sayan dan wasan. Kamar yadda rahoton da kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato, tuni kocin Chelsea Antonio Conte ya ba mahukunta Chelsea umarnin su sayo masa Aubameyang kafin a fara kakar wasa ta bana, tun da ya rasa dan kwallon Everton Lukaku sannan kulob din ba shi da niyyar sabunta kwantaragin dan kwallon gabana Diego Costa da ake ganin zai koma tsohon kulob dinsa Atletico Madrid da ke Sifen.


Aubameyang, dan asalin Gabon kulob da dama ne suke rububin dauke shi kafin a fara kakar wasa ta bana ciki har da wani kulob a Chaina mai suna Tianjin Kuanjian da ya taya shi a kan Fam Miliyan 71 kwatankwacin Naira Biliyan 25 da Miliyan 631 amma dan kwallon bai yanke shawarar komawa can ba. Aubameyang dai ya koma kulob din Dortmund ne a shekarar 2013 kuma ya zura wa kulob din kwallaye 120 a wasanni 189 da ya yi. A kakar wasan da ta wuce ma shi ke sahun gaba a ’yan kwallon da suka fi zura kwallaye a raga a gasar Bundesliga ta Jamus.