✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta fatattaki Graham Potter

Chelsea ce ta 11 a teburin Firimiyar Ingila da maki 38.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fatattaki kocinta, Graham Potter watanni bayan danka masa ragamar horar da ’yan wasanta.

Sallamar kocin na zuwa ne bayan ya gaza tabuka komai inda ko a jiya Asabar kungiyar ta kwashi kashinta hannu bayan Aston Villa ta lallasa ta har gida da ci 2-0 a wasan mako na 29 na Firimiyar Ingila.

A sanarwar da Chelsea ta fitar, ta yi godiya ga tsohon kociyan na Brighton Hove Albion bayan ya maye gurbin Thomas Tuchel.

Chelsea ta ce ba za ta mance da gudunmawar da bayar ba wajen kai kungiyar zuwa wasan daf da na kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai wanda za ta fafata da Real Madrid a tsakiyar wannan wata na Afrilu.

A halin yanzu dai Chelsea ce ta 11 a teburin Firimiyar Ingila da maki 38, inda akwai tazarar maki 34 tsakaninta da Arsenal mai jan ragamar teburin babbar gasar tamaular ta Ingila