✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta fara yunkurin dauke Gareth Bale

Kocin Chelsea Antonio Conte ya fara yunkurin dauke dan kwallon Real Madrid na Sifen Gareth Bale. Kocin, wanda ya dade yana sha’awar Bale ya ce…

Kocin Chelsea Antonio Conte ya fara yunkurin dauke dan kwallon Real Madrid na Sifen Gareth Bale.

Kocin, wanda ya dade yana sha’awar Bale ya ce ya fara tunanin dauke dan kwallon a wannan karo ne ganin yadda kulob din Madrid ya fara yunkurin rabuwa da shi saboda yawan raunin da yake samu.

Sai dai rahoton da wata jarida da ake wallafa ta a Sifen  Don Balon ta kalato an nuna kulob din Chelsea zai iya fuskantar kalubale daga kulob din Manchester United a kokarin dauke dan kwallon.  United tana daga cikin kulob din da suka dade suna zawarcin Bale a baya.

Antonio Conte ya ce zai yi amfanni da kudin da kulob din ya sayar da dan kwallon gabansu Diego Costa ne Fam Miliyan 58 wajen sayen Gareth Bale idan Madrid ta amince ta sayar mata da shi.  Shi dai Diego Costa ya koma tsohon kulob dinsa Atletico Madrid ne, kuma ana sa ran a watan Janairun 2018 zai fara yi wa kulob din kwallo.

Gareth Bale dan shekara 28, yana fama da matsalar yawan jin rauni da hakan ta sa mahukunta Madrid suka fara tunanin cefanar da shi.

Chelsea za ta yi amfani da Bale ne da Morata da kuma Hazard a matsayin ’yan kwallon gabanta da zarar ta saye shi daga Madrid.