✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta fara yunkurin dauke Cabani daga PSG

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Chelsea ya fara tunanin dauke dan kwallon gaba a kulob din PSG na Faransa Edison…

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Chelsea ya fara tunanin dauke dan kwallon gaba a kulob din PSG na Faransa Edison Cabani ganin yadda ya fara samun sabani da Neymar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Chelsea tana kokarin taya dan kwallon ne a kan kudi masu yawa don shawo kan kulob din PSG ya sayar mata da dan kwallon a watan Janairun 2018 idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.

Kamar yadda rahoton ya nuna akwai yiwuwar Cabani ya amince da tayin na Chelsea ganin yadda ya fara samun sabani da Neymar, dan kwallon da ya fi kowane dan kwallo tsada a kulob din da ma a duniya baki daya.

Kocin Chelsea Antonio Conte ya nuna sha’awa a kan Cabani da yake ganin shi zai maye gurbin Diego Costa da ya canza sheka zuwa kulob din Atletico Madrid na Sifen.

Cabani dai ya samu sabani da Neymar ne a bugun fanariti a kulob din PSG a makon jiya al’amarin da ta sa mai kulob din ya yi masa tayin Yuro Miliyan 1 don ya bar Neymar ya rika yin bugun fanariti idan an samu, amma ya ki amincewa da wannan tayi.