✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta dage magoya bayanta hudu saboda cin zarafin Raheem Sterling

A ranar Litinin da ta wuce ce kungiyar Chelsea da ke Ingila ta bayar da sanarwar dage 4 daga cikin magoya bayanta bisa zargin cin zarafin…

A ranar Litinin da ta wuce ce kungiyar Chelsea da ke Ingila ta bayar da sanarwar dage 4 daga cikin magoya bayanta bisa zargin cin zarafin dan kwallon kungiyar Man City da ke Ingila Raheem Sterling.

Jaridar The Mirror ta Ingila ta ce, kulob din ya dauki wannan mataki ne ganin yadda hudu daga cikin magoya bayansa suka rika zagin dan kwallon City Sterling a wasan da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadin da ta wuce, inda Chelsea ta karya lagon City da ci 2-0.

Jim kadan bayan an tashi wasan ne sai Sterling ya gabatar da korafi ga mahukuntan kulob din Chelsea inda nan take kulob din ya gabatar da batun ga ’yan sanda inda suka shiga yin bincike.

Sai dai kawo yanzu ba a gano magoya bayan da suka ci zarafin Sterling ba, amma da zarar an gano su za a dauki mataki a kansu ciki har da dage su daga shiga filin wasan Chelsea don ya zama darasi ga na-baya.

Mahukunta kulob din Man City sun yaba da matakin da kulob din Chelsea ya dauka wajen daukar wannan mataki don ya zama darasi ga saura.