✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Charly Boy ya nemi diyyar miliyan 500 daga rundunar ’yan sanda

Jagoran kungiyar dolacinmu ya isa wacce ake kira Our Mumu Don Do, Charles Oputa wanda ake yi wa lakabi da Charly Boy ya  maka rundunar…

Jagoran kungiyar dolacinmu ya isa wacce ake kira Our Mumu Don Do, Charles Oputa wanda ake yi wa lakabi da Charly Boy ya  maka rundunar ’yan sandan Najeriya a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja inda ya nemi kotun ta nema masa hakkinsa.
Charly Boy ya shigar da karar ne kan zargin tauye hakkinsa na dan adam da ’yancin fadar albarkacin baki da ’yancin taron zaman lafiya a lokacin da aka kai masa hari a zanga-zangar da ya jagoranta a ranar 8 ga watan Agustan.
Karar da Charly Boy ya shigar ta hada da kwamishinan ’yan sandan birnin tarayya na Abuja.
Oputa ya nemi kotun ta ummarci wanda yake kara ya nemi gafara tare da bugawa a jaridu biyar na kasa kuma a biya shi Naira miliyan 100 a matsayin damejin da aka yi masa.
Ya nemi kotun ta umarci wanda yake kara ya biya kimanin Naira miliyan 400 a matsayin damejin da aka yi masa.