✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Charles III: Muhimman Bayanai Kan Sabon Sarkin Ingila

A ranar Alhamis aka ayyana shi a matsayin sabon sarki bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth mai shekara 96.

Babban dan Sarauniyar Ingila, Yariman Wales, Charles mai shekaru 73, ya zamo Sarkin Ingila.

Mutuwar sarauniyar ta zo ne bayan da fadar Buckingham a ranar Alhamis ta sanar da cewa likitocin sun damu da halin da take ciki, tare da ba ta shawarar ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar likita.

Duk ’ya’yanta – Charles da Anne da Andrew da Edward, sun yi tururuwa zuwa wajenta, har lokacin rasuwarta.

Muhimman abubuwa game da Sarki Charles III:

 • Charles ne Yarima Mai Jiran Gado mafi dadewa a tarihin Biritaniya.
 • Shekarunsa na haihuwa 73 kuma ya kasance magaji ga karagar tun yana dan shekara uku kacal, lokacin da mahaifiyarsa ta zamo Sarauniya Elizabeth II.
 • A ranar 15 ga watan Disambar 1948 ne Archbishop na Canterbury ya rada wa Charles suna, a dakin ajiye kayan sauti na fadar.
 • A watan Yunin 1953 Charles ya zama Yarima Mai Jiran Gado na farko a tarihin Birtaniya, wanda ya halarci nadin sarautar mahaifiyarsa.
 • A watan Yulin 1958 ya zamo Yariman Wales na 21, yana da shekaru tara.
 • A 1969 aka fara yi masa tanadin  matsayin Yariman Wales, a wani bikin da aka watsa ta gidan talabijin da aka gudanar a gidan sarauta na Caernarfon, bayan ya shafe wani lokaci a Kwalejin Jami’ar Wales Aberystwyth yana koyon yaren Welsh.
 • A shekara 1970, ya kammala karatun jami’a, wanda ya sanya ya zamo magajin sarauta na farko a kasar da ya yi hakan.
 • A watan Agustan 1979 Sojojin Republican na Irish suka kashe babban kawun Charles kuma aminininsa, Louis Mountbatten.
 • A 1981 ne ya auri Uwargida Diana Spencer a cocin St. Paul da ke Landan, wanda alkaluma suka nuna kimanin mutane miliyan 750 ne suka shaida kulla shi.
 • A watan Yunin 1982 ne kuma Diana ta haifa masa dansa na fari wato yarima William, sai kuma a shekarar 1984  da Yarima Harry ya biyo baya.
 • A ranar 10 ga watan Maris din 1988  Charles ya tsallake rijiya da baya, sakamakon hadari a tseren dusar kankara da ya yi da abokansa a kasar Switzerland.
 • A watan Disambar 1992 Charles da Diana suka ba da sanarwar rabuwarsu, wanda hakan ya girgiza ahalin gidan, musamman na cin amanar aure. Sai dai rabuwar ba ta tabbatar ba, sai a ranar 28 ga Agustan 1996.
 • A watan Agusta 1997 tsohuwar matar tasa Diana, da bazawarinta Dodi Fayed, da direbansu Henri Paul suka mutu a wani hatsarin mota a Paris, yayin da suke kokarin tsere wa masu daukar hoton tsegumi (Paparazzi). Charles ya dage har sai da aka yi mata jana’izar masu rike da sarauta.
 • A ranar 6 ga watan Satumbar 1997 Charles ya raka ’ya’yansu — William da Harry da kawunsu, Charles Spencer, a kafa don raka akwatin gawar Diana makabarta.
 • A watan Afrilun 2005 ya auri masoyiyarsa Camilla Parker Bowles.
 • A watan Maris din 2021 dansa Harry ya caccaki mahaifinsa a wata hira da wani gidan talabijin a Amurka, inda ya koma da zama, bayan datse alaka tsakaninsa da mahaifin nasa a shekarar 2020. Ya kuma zargi Charles da cewa al’ada ta rufe masa ido, kuma har ya cire shi daga jerin wadanda za su gaje shi. Sai dai jami’an masarautar daga baya sun ce ya ware “kudi mai yawa” ga dan nasa.
 • A watan Nuwambar 2021 Charles ya halarci wani biki a Barbados, bayan da tsibirin Caribbean ya zamo jamhuriya.
 • A watan Yunin 2022, matsayin Charles na wanda zai gaji mahaifiyarsa ya kara farin jini a wurin al’umma,  musamman ganin yadda ya wakilce ta a yawancin bukukuwan cika shekaru 40 da 50 a kan karaga.
 • A ranar 8 ga watan Satumbar 2022 ne bayan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II, aka ayyana shi a matsayin wanda ya maye gurbinta — Sarki Charles III, kuma matarsa ​​​​Camilla aka fara kiranta da Sarauniya Consort.