✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CHAN 2018: Yau Najeriya za ta yi wasanta na biyu da Libya

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin Afirka na ’yan kwallon gida (CHAN), a yau ne kungiyar kwallon kafa ta Najeriya za ta…

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin Afirka na ’yan kwallon gida (CHAN), a yau ne kungiyar kwallon kafa ta Najeriya za ta buga wasanta na biyu da Libya.

Idan za a tuna a ranar Litinin da ta gabata, Najeriya ta buga wasan farko ne da kasar Ruwanda kuma suka tashi babu ci wato (0-0).

Sakamakon wasan bai yi wa magoya bayan kwallon kafa na Najeriya dadi ba, ganin cewa kasar ba ta taba lashe kofin wannan gasa ba.

Najeriya dai tana fafatawa ne a rukunin C da kasashen Libya da Ruwanda da kuma Ekuatorial Guinea.

Kawo yanzu Libya ce take samun tebur a rukunin C da maki 3 sai Najeriya mai maki daya sai Ruwanda ita ma da maki daya sai wacce take kasan tebur Ekuatorial Guinea da ba ta samu maki ko daya ba.

Don haka a yayin da Najeriya da ta kece raini da Libya a yau, ita kuma Ruwanda za ta hadu ne da Ekuatorial Guinea.  Za a buga wasan Najeriya da Libya ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya yayin da wasan Ruwanda da Ekuatorial Guinea kuma zai gudana ne da misalin karfe 8 da rabi na dare agogon Najeriya.