✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chadi ta janye jakadanta daga Isra’ila

Chadi ce kasar Afirka ta farko da ta soma daukar irin wannan matakin daga nahiyar Afirka.

Kasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila kiranye sakamakon hare-haren da kasar ke kai wa Gaza.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a ranar Lahadi, ta yi Allah-wadai da irin yadda ake samun asarar rayuka a Gaza tare da kira kan a tsagaita wuta.

Haka kuma ta yanke shawarar yi wa jakadanta kiranye daga Isra’ila zuwa N’Djamena domin tattaunawa.

“Chadi na mayar da hankali sosai kuma ta damu kan abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, musamman tashe-tashen hankulan da ba a taba ganin irinsu ba a Zirin Gaza.

“Sakamakon wannan bala’in, Chadi ta yi Allah wadai da rasa rayukan farar hula da dama tare da neman a tsagaita wuta wanda zai kai ga mafita mai dorewa ga Falasdinu,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, “Dangane da haka ne aka yanke hukuncin yin kiranye ga jakadan da ke Isra’ila domin tattaunawa.”

Da alama Chadi ce kasar Afirka ta farko da ta soma daukar irin wannan matakin daga nahiyar Afirka, duk da cewa tuni kasar Turkiyya ta dauki wannan matakin na yi wa jakadanta kiranye.

Haka ma kasashen Bolivia da Chile da Colombia da ke Kudancin Amurka tuni suka dauki matakin yanke dangantaka da Isra’ilar sakamakon ci gaba da kisan da take yi wa Falasdinawa.

Zanga-zangar kin-jinin Isra’ilar na ci gaba da kankama a kasashe da dama ciki har da Amurka da kuma Birtaniya.

Zuwa yanzu akalla Falasdiniwa 9,970 Isra’ila ta kashe a Gaza, daga ciki 4,800 yara ne kanana, sannan 2,550 mata ne.