✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai tallafa wa manoma dubu 550 da ambaliya ta shafa a a bara

Kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) ta ce, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince zai bayar da tallafi ga manoma shinkafa sama da dubu 550…

Kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) ta ce, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince zai bayar da tallafi ga manoma shinkafa sama da dubu 550 da ambaliyya ta yi wa lalata amfanin gonakinsu a bara.

Shugaban Kungiyar RIFAN ta Kasa, Alhaji Aminu Goronyo, ne ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) haka a Abuja, inda ya ce, Gwamnan Bankin CBN Mista Godwin Emefiele ya ba da umarnin a kara lokacin biyan rancen da manoma suka karba zuwa shekara hudu.

Aminu Goronyo ya ce, “Maimakon biyan rancen a rukuni uku a shekara, an sabunta yadda za a biya rancen a cikin rukuni hudu.” Wadanda suka yi asarar ne kawai za su ci moriyar shirin tallafin na RIFAN/CBN/ABP.

Ya ce, an samu matsaya bayan tattaunawar da aka yi da Daraktan Ci gaban Hada-Hadar Kudi na Bankin CBN da masu ruwa-da-tsaki na Kungiyar RIFAN

Goronyo ya ce, Kungiyar RIFAN ce kadai ta yi zarra wajen taimaka wa manoma, amma suna saran yi wa wadansu manoma rajista a karkashin shirin ba manoman shinkafa rance na Anchor Borrowers Programme (ABP) wanda shirin ya shafe su tare da Bankin CBN, kuma Bankin CBN ya kirkiro shi ne don tallafa wa manoma da suka yi asara lokacin ambaliya, inda  hakan zai taimaka wajen maye gurbin asarar da suka yi.

“Kungiyar RIFAN tana aiki  da Ma’aikatar Gona da Raya Karkara da Fadar Shugaban Kasa da kuma Bankin CBN don tallafa wa wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu kamar yadda Shugaba Muhammadu Bujhari ya yi alkawari,” inji shi.

Kungiyar RIFAN tana bukatar taimako daga Bankin CBN wajen tsara yadda za a karbi rance, wanda hakan zai taimaka wa manoma ta hanyar yaye musu damuwarsu, su koma kamar yadda suke rayuwa kafin ambaliya.

Ya kara da cewa, a wata tattaunawa da aka yi da manoman da suka yi asara a karkashin shirin RIFAN/CBN/ABP da Hukumar Inshorar Noma ta Najeriya (NAIC)  an duba yadda ambaliyar ta bara ta janyo wa manoma asarar dukiyoyinsu.

Kamfanin NAN ya gano cewa, ambaliyar ruwa ta lalata gonakin shinkafa sama da kadadar dubu 100 a Jigawa inda lamarin ya shafi manoman shinkafa dubu 19 a kananan hukumomi 23 da ke jihar.

Sannan a Jihar Sakkwato akalla an samu asarar tan dubu 61 da 197 na shinkafa da kudinta ya kai Naira biliyan 27.5 sanadiyyar ambaliyar ruwan.

Reshen Kungiyar RIFAN, a Jihar Adamawa ya ce, sama da mutum dubu 5 na mambobinta ne suka tafka asara sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a bara.