Sakamakon damuwa da hauhawar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) da hadin gwiwar Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) sun shirya fitar da tan 27,000 na shinkafa mai bawo zuwa ga kamfanonin casar shinkafa a fadin kasar nan.
Wannan wani yunkuri ne na kawar da shingen da ’yan kasuwa ke haddasawa wanda hakan ke shafar farashin shinkafar.
Raba shinkafar kai-tsaye daga dakunan ajiyar RIFAN da ke a jihohi 16 ya zo ne sakamakon karbar shinkafa mai bawo da aka yi dalarta a jihohin Neja da Kebbi da Gombe da Ekiti a matsayin biyan rancen noman da aka bayar karkashin shirin Anchor Borrowers, wacce aka sayar wa masu casar shinkafar, kamar yadda wata majiyar CBN ta sanar.
A wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai na CBN, Nwanisobi, ya fitar ta ce Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele, ya ce: “An zabi Jihar Kaduna ta zama cibiyar da za a kai shinkafar mai bawon a shirin tara shinkafar da ke gudana a sauran jihohin da suka yi zarra a nomanta a bara.’’
A kwanakin baya ne CBN ya kaddamar da dalar shinkafa mai bawo a jihohin Neja da Kebbi da Gombe da Ekiti, inda aka tsara makamancin hakan a Birnin Tarayya da jihohin Ebonyi da Kuros Riba a cikin makonni masu zuwa a wani abu da bankin ya kira gudummawarsa don tabbatar da nomawa tare da samar da wadataccen abinci a Najeriya.
A watan Janairun nan, babban bankin tare da hadin gwiwa da wasu kafofin sun bullo da fitar da kimanin tan 300,000 na masara daga manoman da suka ci gajiyar rancen noma a Anchor Borrowers, matakin da ya sanya ala tilas farashin masarar ya fadi kasa daga N180,000 a kan kowane tan.