✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Castellanos: Dan wasan da ya kafa tarihin shekaru 75 a La Liga

Castellanos, mai shekaru 24, na matsayin aro ne daga New York City.

Dan wasan gaban Girona, Valentin Castellanos ya kafa tarihin sama da shekaru 75 bayan ya zura kwallaye hudu a ragar Real Madrid a La Liga.

Girona dai ta yi raga-raga da Real Madrid mai rike da kambin gasar La Liga a fafatawar da suka yi ranar Talata da 4 -2.

Castellanos shi ne dan wasa na farko da ya ci kwallaye hudu rigis a ragar Madrid a wasan La Liga tun daga shekarar 1947, lokacin da Esteban Echaverria ya ci wa Real Oviedo kwallaye biyar a ragar Madrid.

Dan kasar Argentina Castellanos, mai shekaru 24, na matsayin aro ne daga New York City.

Yanzu haka Real na biye ne da Barcelona da ke saman teburi da tazarar maki 11.