Tsohon golan kungiyar Real Madrid da Spain, Iker Casillas ya sanar da cewa ya yi ritaya daga kwallon kafa.
Tsohon dan wasan, wanda ya kwashe kimanin shekara 22 yana taka leda ya yi ritayar ce yana mai shekara 39, bayan fama da ya yi da jinya tun a watan Mayun bara.
Bayan jinyar, ya dan samu sauki, inda ya fara buga wasa har aka sanya sunansa a cikin ’yan wasan kungiyar Porto na kakar 2019-2020.
Kungiyar Porto ce kungiya ta karshe da ya wakilta kafin ya yi ritaya.
Casillas ya fara tsaron gidan Real Madrid yana karami, inda har ya kai ga kama wa kungiyar wasa 725, inda ya lashe gasar La Liga biyar, da Zakarun Turai guda uku.
A bangaren Spain kuwa, Casillas ya lashe Kofin Duniya sau daya a shekarar 2010, da Kofin Nahiyar Turai guda biyu a shekarun 2008 da 2012.
Bayan komawarsa Porto a shekarar 2015, Casillas ya kama wasa 156, inda ya lashe kofuna guda biyu.