✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Carrick ya zama kyaftin din Manchester United

Kulob din Manchester United na Ingila ya bayar da sanarwar nada shahararren dan qwallonsa Micheal Carrick a matsayin kyaftin din qungiyar.  Bayanin haka na qunshe…

Kulob din Manchester United na Ingila ya bayar da sanarwar nada shahararren dan qwallonsa Micheal Carrick a matsayin kyaftin din qungiyar.  Bayanin haka na qunshe ne a wata sanarwa da kulob din ya fitar a shekaranjiya Laraba a shafin sadarwarsa na Twitter.

Carrick ya zama kyaftin ne bayan tsohon kyaftin din kulob din Wayne Rooney ya canza sheqa zuwa kulob din Eberton don ci gaba da wasa.  Kimanin shekaru 13 kenan da Rooney ya canza sheqa daga Eberton zuwa na Manchester United sai ga shi a wannan lokaci ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

Kawo yanzu Carrick, dan shekara 35 ya yi wa kulob din Manchester United wasanni har sau 479 yayin da ya yi wa qasarsa Ingila wasanni 34.

A watan Yulin 2006 ne Carrick ya canza sheqa daga kulob din Tottenham zuwa na United, kuma tun daga wancan lokaci kimanin shekaru 11 kenan ya samu nasarar lashe kofuna a kulob din United ciki har da kofuna biyar na gasar firimiyar Ingila.