✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cape Verde da Senegal sun yanki tikitin zagaye na biyu a Gasar AFCON

Yanzu Senegal da ke rike da kofin tana mataki na ɗaya a rukunin C da maki shida.

Tawagar kwallon kafar Cape Verde ta yanki tikitin tsallakawa zagaye na biyu a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka wato AFCON.

Wannan dai na zuwa ne bayan nasarar da Cape Verde ta yi da kwallaye 3 da nema a wasan ranar Juma’a da ta fafata da Mozambique.

Nasarar dai ta bai wa Cape Verde damar ci gaba da zama jagorar rukuninta na B da maki 6 bayan nasara a dukkanin wasanninta biyu.

A karawarta ta farko, Cape Verde ta doke Ghana ne da kwallaye 2 da 1, inda a yanzu ta ke matsayin tawaga mafi samun nasara a rukuninta.

Nasarar ta Cape Verde ta sanya sauran tawagar kasashen rukunin 3 da suka kunshi Masar da ke matsayin ta 2 da maki 2 kana Ghana a matsayin ta 3 da maki 1, sai Mozambique da maki 1 a tsaka mai wuya.

Rukunin na B dai na sahun rukunnai mafiya tarnaki a gasar ta AFCON wadda kasashe 24 ke fafatawa don lashe kofin da yanzu haka ke hannun Senegal.

Senegal ta bi sahun Cape Verde 

Senegal ta bi sahun Cape Verde, inda ta zama kasa ta biyu da ta tsallaka zuwa matakin rukunin ‘yan 16 a Gasar AFCON da ke ci gaba da gudana a Ivory Coast.

Senegal wadda ke kare kambin AFCON ta doke Kamaru da ci 3-1, kazalika a wasan farko ma ta doke Gambia da ci 3-0.

Yayin wasan ranar Juma’a wanda ya gudana a filin wasa na Yamoussoukro, Senegal ta fara zura kwallo a minti na 16 da fara wasa ta hannun Ismaila Sarr, kana Habib Diallo a minti 71, koda yake Kamaru ta farke a minti na 83 ta hannun Jean-Charles Casteletto.

Bayan karin lokaci ne Sadio Mane ya zura kwallo a minti na 95 , wanda ya bai wa tawagar karkashin jagorancin Aliou Cisse damar nasara a wasan da kwallaye 3 da 1.

Yanzu Senegal da ke rike da kofin tana mataki na daya a rukunin C da maki shida, Guinea na biye mata da maki hudu a matsayi na biyu.

Kamaru na matsayi na uku da maki daya yayin da Gambia ke ta ƙarshe ba tare da maki ko ɗaya ba.