✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin shekar siyasar Jigawa:- Ba wani abin labari a tarihin Jihar

Tun bayan da babbar jam`iyyar adawa ta APC, ta yi nasarar lashe zabubbukan kasar nan a babban zaben da ya gabata a watan Maris da…

Tun bayan da babbar jam`iyyar adawa ta APC, ta yi nasarar lashe zabubbukan kasar nan a babban zaben da ya gabata a watan Maris da Afrilu a kasa da wasu jihohi ake ta samun jiga-jigan Jam`iyyar PDP da ta yi mulkin kasar tunda aka dawo harkokin wannan Jamhuriyya ta Hudu da suke ta kaurace wa jam`iyyar zuwa Jam`iyyar APC, tamkar wani sabon yayi a yi haka din. Koda a Jihar Bayelsa, wadda ita ce jihar haihuwa ta tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a kwanakin baya sai da aka samu wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC, haka labarin yake a jihohi da dama da PDP din ta dade tana mulki, tun kafa jamhuriyyar da muke ciki a 1999, irin su Neja da Katsina mahaifar Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari mai ci yanzu da dai sauran jihohi. Wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP din da suke da rabon ba za su shiga jerin wadanda za a yi ta tereren sun zama butulu ba, irin su tsofaffin mataimakan gwamnonin jihohin Jigawa Alhaji Ahmed Mahmud Gumel da na Neja Alhaji Musa Ibeto, tun ba a kai ga fara zabubbuka ba suka yi ban-kwana da jam’iyyarsu ta PDP, suka canja sheka zuwa APC, wasu kuma kamar yadda na ambata sai bayan da nasara ta tabbata, suka koma cikin Jam’iyyar APC, wasu kuma suna kan hanya.
  Ana alakanta wannan canjin shekar ’yan siyasa a wannan zamani da ba babba ba yaro da cewa tana faruwa ne a kan rashin AkIDA da MANUFA a siyasar wannan jamhuriyyar, sabanin siyasar Jamhuriyar ta Farko daga 1960 zuwa 1966, da aka kafa kuma aka yi a kan AkIDA da MANUFA da neman ’YANCI, amma ba wai don neman abin duniya ba, kamar yadda masu yin ta yanzu suke kiranta, KASUWAR BUkATA.
  Makalar tawa ta yau za ta mayar da hankali ne a kan labarin da ke ta yawo a Jihar Jigawa da ma kasa baki daya, cewa wasu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka dana gwamnati tare da Alhaji Sule Lamido na tsawon shekara takwas, wadanda da ma Alhaji Sule Lamidon gadarsu ya yi daga Gwamnatin Alhaji Saminu Turaki ta 1999 zuwa 2007, wai suna shirin komawa Jam’iyyar APC, wato ma’ana za su bi sahun tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ahmed Mahmud Gumel da wasu da suka koma APC, tun kafin a fara zabubbukan bana. Wadanda ake zargin za su canja shekar, sun hada da tsohon dan Majalisar Wakilai tun a 1999, yau shekaru 16, Alhaji Bashir Adamu Kazaure da Alhaji Lawan danzomo, tsohon Kwamishina a Gwamnatin Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, a baya-bayan nan kuma Mashawarci na musamman a Gwamnatin Alhaji Sule Lamido da Alhaji Hassan Malam Madori, shi ma tsohon Mashawarci a Gwamnatin Alhaji Ibarhim Saminu da kuma a Gwamnatin Alhaji Lamido, sai kuma Alhaji Muhammadu Daguro Hadeja da Alhaji Bala Sifiyanu Jahun shi ma jigo a cikin tafiyar Gwamnatin Alhaji Saminu da Alhaji Sale Taki tsohon shugaban karamar Hukumar Kazaure, dan ga-ni- kashe-nin Alhaji Lamido da kuma tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar mai shekara 16, yana wakilci, Alhaji Yahaya Bigman da kuma wasu shugabannin kananan hukumomi masu mulki 15. Ana ma zargin wasu na kan hanya.
Daga bangaren wadanda ake zargin za su canja shekar har yanzu ba wanda ya bayyana a kafofin yada labarai da ya tabbatar wa duniya aniyar tasu, amma a tattaunawar da na yi da wani daga cikinsu ya tabbatar mini da cewa lallai kam akwai waccan aniya, har ma ya kara mini haske da cewa Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya neme su kan wannan bukata, kuma suna nan suna tattaunawa da Gwamnan. Amma shi shugaban Jam’iyyar PDP a jihar Alhaji Muhammadu Kuit da aka tuntube shi, cewa ya yi ba shi da labarin wancan yunkuri daga jiga-jigan jam’iyyarsa. Shi kuwa tsohon mai ba tsohon Gwamna Lamido shawara a kan harkokin matasa Kwamared Umar danjani Hadeja cewa ya yi lallai akwai wancan yunkuri daga wasu ’yan jam’iyyarsu, har ma ya kara da cewa “Lamido ya fada musu cewa suna da ’yancin su yi hakan, idan har ba za su iya jure wa zaman shekara hudu ba gwamnati ba. Ya tunatar da su tare da gargadinsu cewa lallai za su yi nadamar abin da za su yi nan gaba,” in ji Kwamared danjani.
Amma wanda muka tattauna da shi daga cikin masu shirin kaurace wa PDP din da na tunatar da shi jan hankali da tsohon Gwamna Lamido ya yi musu, ya tabbatar mini da cewa tsohon Gwamnan yana da damar ya fadi abin da ya fadi, kuma sun ji. Shi kuwa Gwamna Badaru Abubakar da ya tabbatar da wannan yunkuri na wasu jiga-jigan ’yan Jam’iyyar PDP na komawa jam’iyyarsa ta APC, a wata tattaunawa da manema labarai a cikarsa kwana 100 a kan karagar mulkin jihar, cewa ya yi jiga-jigan PDP din da za su canja sheka, za su yi haka ne bisa ga gamsuwa da irin salon mulkinsa na yin komai a bude, tare kuma da sa hannun kowa da kowa, inda ya ba da tabbacin cewa suna aiki tare cikin fahimta da mutunta juna shi da dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar 27, ba tare da ya sauke ko dayansu ba.    
Idan har canjin shekar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC, walau a kasa ko a wasu jihohi ya zama sabon labari, a Jihar Jigawa bai kamata ya zama sabon labari ba, domin kuwa tunda aka kafa jihar ta Jigawa a watan Agustan 1991, tauraruwar mutane biyun da ake ganin tana haskawa a siyasar jihar, inuwar siyasa daya suka fara zaman sha, wato rushashshiyar Jam’iyyar SDP. Ga wadanda suka manta ya kamata su tuna, lokacin da Alhaji Ali Sa’ad Birnin Kudu Gwamnan farko na farar hula a jihar yake Gwamna 1992 zuwa 1993, a inuwar Jam’iyyar SDP, Alhaji Lamido yana Uban jam’iyya, Alhaji Saminu ke shugaban jam’iyyar reshen jihar ta Jigawa, har zuwa watan Nuwambar 1993 da tsohon Shugaban kasa marigayi Janar Abacha ya rusa tafiyar Jamhuriya ta Uku.
Da aka dawo wannan jamhuriyar a 1999, Alhaji Lamido ba su sha inuwar siyasa daya da Alhaji Saminu ba, yayin da Alhaji Lamido ya fada Jam’iyyar PDP, Alhaji Saminu ya shiga Jam’iyyar APP, kuma dukkan jam’iyyun nasu biyu sun tsaida kowannensu ya zama dan takarar neman mukamin Gwamnan Jihar ta Jigawa a shekarar 1999, inda Alhaji Saminu ya kada Alhaji Lamido, haka aka maimaita a zaben shekarar 2003, duk da Alhaji Lamido bai tsaya takara ba, amma dai Alhaji Saminu ya sake yin nasara a kan dan takarar Jam’iyyar PDP. A zaben 2007, Alhaji Saminu ya ja mafi yawan mutanensu suka canja sheka zuwa Jam’iyyar PDP, kuma bisa ga kaddara ya mika takarar neman mukamin Gwamnan Jihar ga Alhaji Lamido, kuma Allah Ya ba da nasara. Da dadi ba dadi an zauna shekara takwas ris, da Gwamna Lamido da mutanen Alhaji Saminu wadanda suka bi tafiyar canjin shekar tun farko sai abin da ba a rasa ba, duk kuwa da zaman doya da man jan da aka yi ta yi tsakanin Gwamna Lamido da tsohon Gwamna Saminu.    
Shi kansa sabon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar, amini ne na kut-da kut, da aka yi Gwamnatin Alhaji Saminu da shi, kuma ba ya da tarihin ya taba yin Jam’iyyar PDP ko mai kama da ita, duk da yake ya taba  yi wa DPP takarar neman mukamin Gwamnan Jihar ta Jigawa. Don haka mene ne sabon labari a siyasar ta Jigawa idan har wadancan mutane sun CANJA sheka sun bar PDP yanzu?