Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar JIBWIS reshen Jihar Kaduna, Sheikh Aliyu Abdullahi Telex, ya jawo hankalin mahukunta a Najeriya da su ji tsoron Allah su sake tunani bisa halin da al’umma ke ciki a sanadiyyar sauya fasalin takardun kudi.
Sheikh Aliyu Telex ya yi wannan kira ne a hudubar Juma’a da ya gabatar a Masallacin Juma’a da ke Tudun Jukun a Zariya.
- Ukraine ta lalata wa Rasha makamai masu linzami biyar
- Canjin Kudi: Ganduje ya maka Buhari a Kotun Koli
Ya ce ya zama wajibi su fadakar tare da yin kira ga mahukunta su gaggauta kawo karshen kuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke ciki na matsin tattalin arziki da canjin kudi ya jefa su.
Babban Limamin ya kuma gargadi mahukunta da kar son zuciya ya kai su ya baro har hakan ya tunzura al’umma su yi wa gwamnati bore.
Ya ce, duk talaka mai jin yunwa ba abinda ya ke so sai abinci saboda haka ya zama wajibi ga mahukunta a kasar nan su yi wa kansu karatun ta natsu kafin tura ta kai bango.
Sheikh Aliyu Telex ya kuma bayyana cewa karin lokacin canjin kudin da aka yi bai amfani kowa ba saboda babu kudin ma a bankunan.
“Ya mutum da kudinsa amma na hidimar gida ya gagareshi duk da cewa har kwana a kan samu wasu na yi a layin cirar kudi ta na’urar ATM.”