Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya maka Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Kotun Koli kan sauya fasalin da aka yi wa takardun naira.
A watan Oktoban bara ne dai Babban Bankin Najeriya CBN bisa amincewar Shugaba Buhari ya sauya fasalin wasu daga cikin manyan kudin kasar na naira 200 da 500 da 1,000.
- APC ta dage yakin neman zaben shugaban kasa a Kano
- Kotu ta kori Mohammed Abacha daga takarar gwamnan Kano
A karar mai lamba SC/CS/200/2023 wadda Babban Lauyan Jihar Kano ya shigar ta hannun Sunusi Musa, Babban Lauya a Najeriya (SAN), Gwamnatin Kano ta ayyana cewa Shugaba Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar CBN dakatar da tsoffin takardun kudin da aka sauyawa fasali
Aminiya ta ruwaito cewa, karar wadda Gwamnatin Kano ta gabatar a jiya Alhamis, ta kafa hujjar cewa Buhari ba shi da wannan hurumi ba tare da tuntuba da amincewar Majalisar Tattalin Arziki da kuma Majalisar Zartarwa ta kasar ba.
A bisa wannan madogara ce Gwamnatin Kano ta bukaci Kotun Kolin ta soke matakin Babban Bankin na janye takardun kudaden saboda abin ta kira wahalar da al’ummar jihar ke ciki.
A tattaunawarsa da manema labarai, Babban Lauyan da ya shigar da karar Sunusi Musa ya ce a ranar Laraba ne kotun za ta saurari karar.
Kazalika, Gwamnatin Kanon tana son kotun ta bayar da umarnin da zai tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta soke shirin nata na sauyin kudi saboda a cewarta ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Kasar na 1999.
An kuma ruwaito cewa Gwamnatin Kanon tana bukatar Kotun Kolin ta zartar cewa umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa CBN na takaita yawan kudin da jama’a za su fitar daga asusunsu na banki ba tare da tuntubar Majalisar Tattalin Arziki da kuma ta Zartarwa ba, abu ne da ya saba wa tsarin mulki da saba wa doka a don haka ba shi da iko.