Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ya ce yaudarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya yi har ya amince da sauyin takardun kudi.
Oshiomhole ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a shirin Daily Politic na Gidan Talabijin din Channels.
- Adadin mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiyya da Syria sun zarta 1300
- An binne gawarwakin mutum 71 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina
A cewar Oshiomhole, Gwamnan CBN din ya yi amfani da akidar Shugaban Kasa ta yaki da cin hanci da rashawa wajen cusa masa tsarin.
Shugaban APCn ya kuma ce zargin zagon-kasa da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi a baya-bayan nan kan akwai wasu makusantan Buhari da ke yi wa dan takararsu Bola Tinubu gaskiya ne.
“Babu wata hikima a sauya takardar kudin nan da aka yi.
“CBN yaudarar Buhari ya yi, domin manufarsu shi ne hana gudanar da zaben ma baki daya.
“Kasancewata shugaban jam’iyya, na samu damar yin aiki kai tsaye da Shugaba Buhari, kuma ina mai tabbatar muku da cewa dabara ce Emefiele ya yi wa Shugaban Kasa.
“Na kadu matuka da wannan shirme na CBN, domin ko a zamanin mulkin soja da Buhari ya canja takr6dun kudi, bai hana bankuna bai wa mutane kudi ba, bai kuma takaita musu nawa za su cire ba tunda kudinsu ne,” in ji Oshimhole.
Tsohon Shugaban APCn ya kuma ce: “Ina ganin abin da El-Rufai ke cewa shi ne idan kana ta samun zanga-zanga daga ko’ina a kasa, abinda zai faru shi ne dole ka dakatar da gudanar da zabe saboda babu zaman lafiya.”