Shugaba Buhari na jagorantar taron Majalisar Koli ta Kasa domin tattauna batutuwan da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
A na sa ran taron Majalisar da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa zai tattauna kan matsalar mai, sauyin kudi, karancin takardun Naira da kuma sha’anin tsaro gabanin babban zabe da za a yi nan da mako biyu.
- Yadda karancin kudi ya karya farashin abinci a kasuwanni
- Canjin kudi zai shafi ayyukan sojoji —Monguno
Taron ya samu halarcin tsoffin shugabannin kasa irin su, Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, da kuma Yakubu Gowon da gwamnoni da kuma Shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa.
Majalisar Koli ta Kasa wani bangare ne Gwamnatin Najeriya da ke ba da shawarwari kan tsare-tsaren gwamnati a bangaren zartaswa.
Mahalarta zaman na ranar Juma’a sun hada da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Ministan Shari’a da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da .
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da sauransu na daga cikin mahalarta zaman.