✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Canja shugabancin Bankin Skye ba zai shafi kudin masu ajiya ba’

Babban Bankin Najeriya wato (CBN) ya nada sabon shugaban Bankin Skye bayan ya karbe ikon tafiyar da bankin saboda gazawar bankin wajen cika sharuddan da…

Babban Bankin Najeriya wato (CBN) ya nada sabon shugaban Bankin Skye bayan ya karbe ikon tafiyar da bankin saboda gazawar bankin wajen cika sharuddan da CBN yake gindaya wa bankunan kasar nan.
A ranar Litinin ne CBN ya sanar da rushe kwamitin gudanarwar bankin, inda ya dakatar da shugaban bankin da mataimakinsa yayin da wasu daga cikin daraktocinsa suka sauka daga mukamansu bisa radin kansu.
Gwamnan CBN Godwin  Emefiele wanda ya yi sanarwar ya ce Bankin Skye ya kasa cika wasu tanade-tanade da CBN ya bukace shi, “inda a lokaci mai tsawo CBN yake binsa bashin wasu makudan kudi da ya kasa biya.”
Daga nan ne sai gwamnan ya sanar da nadin Alhaji Muhammad K. Ahmad a matsayin sabon shugaban bankin, yayin da Mista Adetokunbo Abiru aka nada shi sabon manajan daraktansa.
A wata sanarwa da Bankin Skye ya fitar, ya ce bankin ba ya cikin mawuyacin hali, don haka jama’a za su iya ci gaba da hulda da shi ba tare da fuskantar wata matsala ba.
An sauke shugabannin bankin ne saboda rigakafin kada ya fada cikin matsala. Gwamnan ya ce “Canja shugabancin Bankin Skye ba zai shafi kudin masu ajiya ba.”