Idan hikima da kyau da camfi da tarihi suna bukatar a ba su suna irin na kimiyyar sanin tsirrai, to fa “Adansonia digitate,” ko katafariya, sannan tsohuwar itaciyar kuka da ta kafu ta kuma yadu a daukacin yankin Kudu da Saharar Afirka mai tsandauri, ta cancanci wannan girmamawa.
Itaciyar kuka wadda ta samo asali daga nahiyoyin Afirka da Austireliya, tana dauke da siffofin da suka dace da yanayin Afirka na tarihi, tare da kasancewa alama ga wasu al’adu da wasu suka yi imani da su.
Itaciyar rayuwa ce ta hanyoyi da dama, da suka hada yanayin zamantakewa da al’adun dan Adam da suka shafi tarihin dan Adam musamman a Nahiyar Afirka da ta yi zurfi cikin kimiyya da camfecamfe.
A cewar yarjejeniyar Majalisar dinkin Duniya kan yaki da hamada, itaciyar kuka “Za ta iya rayuwa tsawon shekara 3,000, kuma girman fadinta na iya kaiwa mita 50 sannan tsayinta na iya kaiwa mita 30.”
Tana da nau’o’i daban-daban har tara, shida daga ciki na iya tsirowa a Tsibirin Madagaska na Afirka, itaciyar kuka ta kasance abar nazari da bincike da kuma kwatance. Daga cikin fitattun irin itatuwan kuka da ake da su a duniya, akwai Sagole Baobab na Afirka ta Kudu, wacce ta rike kambun duniya na ‘Guiness World Record’.
A harshen Hausa ana kiran Baobab kuka, Reniala a harshen Malagasy, da kuma Mbuyu da harshen Swahili.
Sunan itaciyar kuka, Gouye Gui a harshen Wolof, a harshen Lingala kuma sunanta Zelo. A al’adun gargajiya wasu na kiran itaciyar kuka a matsayin jirkitacciyar itaciya. Yanayinta da ke a karkace, lamarin da ya sa tamkar tushenta na kokarin komawa sama.
Wani suna da ake kiran wannan itaciya da shi wanda ba a saba da shi ba shi ne, “cream of Tartar tree” – abin da ke nufin, rufaffen kwanson da ke jikin itaciyar.
Wannan kwanso ya kunshi wani sinadarin acid mai tsami wanda za a yi amfani da shi wajen hada madara da samar da sinadaran dafa abinci da yin burodi da kuma giya. bacewa a hankali Kuka itaciya ce mai ban-mamaki da ke girma a birane, kauyuka da kuma daji.
Itaciyar na cikin mafiya girma kuma mafiya dadewa a duniya. Kama daga Madagaska da Afirka ta Kudu da Zimbabwe zuwa Senegal da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Najeriya, jerin itatuwan kuka suna kawata yanayin Afirka. A kimiyyance, duk da itaciya ce mai laushi, an tabbatar da cewa kuka na jure cin wuta, “Sai dai in ta mutu ko kuma ta bushe.”
“Itaciyar ba ta ci da wuta’’ in ji Dokta Mustapha Karkarna, kwararre a fannin kula da gandun daji da ke Jami’ar Bayero, Kano, yayin zantawa da TRT Afirka ta yi da shi. “Kasancewar kuka wata dadaddiyar alama ce ko shaida a wurin da mutane ke zama, tana da amfani da yawa wajen yin magani da sana’a.
“A yanayi da ilimin muhalli, tana da daraja, hakan ya sa ba kasafai mutane suke sare itaciyar kuka ba. Tsuntsaye na son itaciyar don irin kariyar da take bayarwa ga gidajensu da suke sakawa,” in ji shi.
Sai dai a gargadin da Garba Sani, wani mai daukar shiri na bidiyo, ya ce a Arewacin Najeriya, yawan itaciyar kuka na bacewa sannu a hankali daga birane. “Idan aka yi la’akari da irin griman gangar jikinta, ana ganin kuka a matsayin itaciya mai mamaye wuri musamman ta fannin masu gine-gine,” in ji shi.
Sani ya koka kan yadda sababbin masu inganta filaye ke saurin yanke manyan itatuwan kuka, wanda hakan ke haifar da raguwarsu a birane. Nyasha Chibanda, haifaffen kasar Zimbabwe kuma kwararre a fannin ci gaban kasa-da-kasa, da ke zaune a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, ya yi wani sharhi na daban.
“A Lardin Masbingo da ke gabashin Zimbabwe, galibin itaciyar kuka na girma ne a yankunan karkara da ke da wurare masu fadi da yalwa. Mazauna wajen ba su ga dalilin da zai sa a yanke itatuwan kuka ba.” Dimbin amfaninta Bayan kasancewarta wata alama ta al’adu a Afirka, yaduwar kuka a nahiyar ta kasance abar fiffiko saboda amfaninta na da muhimmanci sosai wajen zama matsuguni da abinci mai gina jiki da samar da waraka ta hanyar magani.
Baya ga wasu manyan nau’o’in itatuwa da ake da su, itatuwan kuka na zama tamkar muhalli kasancewar tushensu na zuwa can kasa ya rike kansa maimakon ya gangaro ya iya lalata gine-gine.
Abdulkadir Musa, wani malami mai ritaya a garin Giyade da ke Jihar Bauchi a Arewa maso Gabas, ya yi kari haske a kan muhimmancin da kuka take da shi ga muhallin yankunan.
Imani na gargajiya
Daga filayen noma zuwa gidaje, kuka tana taimakawa wajen takaita zaizayar kasa, kuma manoma ba sa ganin wani lahani daga gindin itaciyar da ke zama inuwa kuma ke taimaka wa amfanin gona. Sani ya ce a kasar Hausa sunayen wasu wuraren suna bin wata itaciyar kuka ce da ke asali a wajen ko kuma ta taba kasancewa.
“A tsohon birnin Kano, akwai wurare kamar Kuka Bulukiya da Kuka Uku, sannan akwai Kukar Atillo a garin Nahuce da ke Taura a Jihar Jigawa,” in ji shi.
A fagen al’adun Afirka, ana samun kuka a ko’ina, wasu kuma sun ce ta mamaye ko’ina. Ana yaba mata a wasu al’ummomi saboda yadda ake amfani da ita a gargajiyance wajen maganin wasu cututtuka.
Akasin haka, kuka ta yi kaurin suna a wasu al’adun a matsayin itaciya mai mugun abu. Wasu addinai a Afirka suna danganta nau’in da dubban tsafi kamar su bautar kakanni da addu’o’i da ake yi na tsibbu da aljanu da dai sauransu. A wasu al’ummomi kuwa ana daukar kuka a matsayin “itaciyar da ba a samun ta a cikin gari.”
Jure wa kowane yanayi
Al’adun Hausawa kafin zuwan addinin Musulunci, suna kallon itaciyar kuka a matsayin mazaunin aljannu, kuma ana gargadin yara su guji hawa ko wasa da itaciyar domin hadarin shigar aljannu jikinsu. Shahararriyar kungiyar bori ta rayerayen Hausa tana nuna kuka a yawancin ayyukanta.
Kirar itaciyar kuka na bayyana ne tamkar wata tsohuwar katangar tsaro.
Itaciyar na iya zama matacciya bayan ta zubar da ganyenta, amma da sauri take farfadowa tare da bayyanar ’ya’ya da ganyayyaki ta dawo rayuwa tare da kyalli. Yanayin juriyar itaciyar kuka na ba ta damar ci gaba da yin ’ya’ya koda kuwa ta fadi, muddin akwai wasu saiwoyi da suke manne a kasa.
“A bangaren itaciyar kuka da ke kai ruwa zuwa ganyayyakinta daga saiwoyi da kuma wanda ke saukar da ruwa zuwa ga saiwoyin a hade suke, abin da ya sa karancin ruwa ba ya mata barazana,’’ in ji Dokta Mustapha Karkarna, tsohon Shugaban Shirin Kula da Albarkatun Gandun Daji na Jihar Kano.
Itaciyar takan kuma mallaki manyan koguna da ramuka inda dabbobi masu rarrafe da beraye da tsuntsaye suke fakewa.
A cewar Dokta Karkarna, wasu nau’o’in cututtuka dangin fungal ne ke haifar da ramuka a itaciyar kuka ba wani abu da ya saba hankalin dan Adam ba.
Dokta Karkarna ya yi imani cewa babban abin da ya sa ake camfi a kan kuka shi ne kasancewar itatuwan sun kasance cikin tsirrai mafiya dadewa a duniya.
Itaciya daya tana iya girman mutum mafi tsufa a cikin al’umma gaba daya. Don haka, ana daukar su a matsayin shaidun abubuwan da suka gabata, kuma suna da labaran da za su ba da na tarihin al’umma.
Yayin da itaciyar ke girme wa al’umma, tana dauke da alamar tsawon rai da hikima, abin da ya sa mutane suke mata fassarori masu nasaba da makabarta da kuma aljanu.
Abin da ke sa a bayyana ta a matsayin wata alama ta mugun abu a cikin tatsuniyoyi da camfe-camfe Wata babbar barazana ga wanzuwar kuka duk da muhimmancinta a yanayin Nahiyar Afirka da al’adu daban-daban shi ne fadadar birane da fifita tsirrai baki fiye da nau’o’in na Afirka. Amma kamar yadda masanin falsafar Jamus, Friedrich Nietzsche ya ce, dole a sha wahala idan za a rayu, batun kawai shi ne a samu ma’ana cikin wahala.
Babu wani abu da watakila ya kwatanta wannan al’amari fiye da dadaddiyar itaciyar kuka da ta rayu a karnin da dan Adam ke ci gaba da bunkasa da kuma barnatar da kewayensa.
Ana gane wanzuwar biranen Hausawa daga kukoki
Hakika, kasancewar tunda jimawa, babu shahararrun gine-gine masu kafuwa cikin kasa a kasar Hausa, muna iya cewa babu wani ma’auni da ke tabbatar mana da wanzuwar tsohuwar rayuwa a kasar Hausa sama da rukunin kukoki.
Ko tantama babu, duk inda aka samu kukoki sun jeru reras, ko sun yi da’ira, ko wani abu mai kama da haka, to akwai labarin cewa gari ya taba wanzuwa a wannan wuri. Ana sanin tsufan gari gami da tumbatsarsa daga kukoki.
Tsohuwar alakar Hausawa da iskokai A da, hasashe ya fi tafiya a kan cewa mu’amala da iskokai ke tilasta wa Hausawan dauri rayuwa da kukoki a muhallansu Kasancewar itaciyar kuka na daya daga cikin itatuwan da iskokai ke zama a samansu har ma akan ce sarakunan aljannu da yawa sun fi yin fadojinsu a kan itaciyar kuka, don haka akwai alamun jimawar alaka a tsakanin Hausawa da wadancan iskokai.
Mun sani sarai kafin zuwan Musulunci kasar Hausa ana rayuwa ce irin yanayin mai karfi shi ke da iko. Don haka kusan kowane mutum na zamanin yana kokarin rikar wani abu na camfi mai jibi da iskokai wadanda zai rika ba shi kariya a duk lokacin da bukata ta taso, tare kuma da samun biyan bukatarsa.
Don haka akwai yiwuwar wannan camfi ne silar da kusan daukacin Hausawan dauri suke shuka itaciyar kuka a muhallinsu domin samun wata kariya daga makarai.
Zuwa yanzu dai, akwai itatuwan kuka birjik a daukacin tsofaffin biranen kasar Hausa, kuma akwai labarai da yawa kan yawa-yawan manyan kukokin cikinsu, ta yadda wasu ma za ka ji har sunaye aka ba su.
Ga kadan daga sunayen itatuwan kuka masu dauke da wani labari a kasar Hausa: Kukar Boka, Kukar Gajere, Kukar Mai Rabo, Kukar Allah Ya isa, Kukar Kwandi, Kukar Karaya, Kukar Bulukiya, Kukar Jarmai, Kukar Makuwa da sauransu.
Amma fa, muna iya cewa har yanzu akwai karancin sani gare mu dangane da ainihin alakar kukoki da Hausawa.
Sadik Tukur Gwarzo ya rubuta wannan nazari ne a Aminiya tare da karin bayani daga rubutun shafin TRT Afirka.